Labarai
Shugaba Tinubu Ya Nada Jega Mai Ba Shi Shawara Na Musamman Kan Harkokin Kiwon Dabbobi
Shugaba Bola Tinubu ya nada tsohon Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, Farfesa Attahiru Muhammadu Jega a matsayin mai ba da shawara na musamman kan sake fasalin kiwon dabbobi.
Shugaban ya yi fatan nadin Farfesa Jega zai haifar da ci gaba mai ma’ana a fannin kiwo, da kuma kara karfafa ayyukan ci gaban kasa.
Tsohon Mataimakin Shugaban Jami’ar Bayero ta Kano, Farfesa Jega ne ya jagoranci Kwamitin Kiwo na Shugaban Kasa tare da Shugaba Tinubu.
Wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan yada labarai Bayo Onanuga ya fitar, ta ce kwamitin ya bayar da cikakkun shawarwarin da suka tabbatar da sauye-sauyen da aka samu a fannin kiwon dabbobi, daya daga cikinsu shi ne samar da ma’aikatar kiwo.
Jega, mai shekaru 68, mamba ne a Majalisar Ba da Shawarar Zabe ta Duniya, kuma Shugaban Majalisar Gudanarwa na Jami’ar Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Jihar Kano.
Ya rike mukamin shugaban hukumar ta INEC tsakanin shekarar 2010 zuwa 2015.
Sanarwar ta ce nadin nasa zai karfafa nasarorin da kwamitin shugaban kasa ya samu, tare da tabbatar da ci gaba da sauye-sauyen da aka fara gudanarwa.
Daga Bello Wakili
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
