Labarai
Sheikh Daurawa Ya Amince Da Cigaba Da Jagorantar Hukumar Hisbah
Kwamandan Hisbah ta jihar kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya dawo mukaminsa bayan sulhun da kungiyar Inuwar hadin kan malaman Kano ta jagoranta tsakanin sa da gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf.
Idan za’a iya tunawa a ranar Juma’a ne Sheikh Daurawa ya bayyana Ajiye mukamin nasa bayan wasu kalamai da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya yi, inda ya Kalubalanci yadda hukumar take gudanar da wasu daga cikin aiyukan ta.
Da yake zantawa da Manema labarai Mai magana da yawun gwamnan jihar kano Sanusi Bature Dawakin Tofa yace an sami mahimtar junan ne a wani zama da da aka yi tsakanin zauren malaman kano da Sheikh Daurawa da kuma gwamna Abba Kabir Yusuf.
Yace “dama tun da farko a wajen gwamnati Malam bai ajiye aikinsa ba, saboda bai rubuta ba , don haka Ina tabbatar da cewa an sami masalaha kuma malam zai cigaba da yin aikinsa yadda ya kamata.
A wani rubutaccen jawabi da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya tabbatar da yin sulhu a dare wannan rana ta Litinin.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
