Labarai
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Ya Raba Tallafin Ramadan A Mazabarsa
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Yusuf Dahiru Liman, ya raba kayayyakin agaji na watan Ramadan na sama da Naira miliyan 200 ga al’ummar mazabarsa.
Ya yi hakan ne da nufin tallafa wa al’umma domin samun damar gudanar da azumin watan Ramadan cikin sauki, duba da halin da ake ciki na tabarbarewar tattalin arziki.

A wajen bikin kaddamar da rabon, Yusuf Dahiru Liman, wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatan ofishinsa, Bashir Adamu Nababa, ya jaddada aniyarsa ta rage wahalhalun da al’ummar mazabarsa ke fuskanta.
Ya bayyana rabon kayayyakin a matsayin wani bangare na alkawarin da ya dauka na inganta walwalar jama’a a yayin yakin neman zabe.
Shugaban kwamitin masu ruwa da tsaki, Isiyaku Adamu Nababa, ya jaddada cewa shirin ya nuna irin sadaukarwar da shugaban majalisar yake yi na yi wa al’ummarsa hidima baya ga ayyukan majalisa.
Ya bayyana sauran ayyukan jin kai da Yusuf Liman ya jagoranta, da suka hada da ayyuka a fannin ilimi, da kiwon lafiya, da kuma sanin makamar aiki.

Da yake jawabi a wajen taron, Hakimin Barnawa, Alhaji Kabiru Zubairu, ya bayyana jin dadinsa bisa jajircewar da kakakin majalisar ya yi wajen kyautata rayuwar al’ummar mazabarsa.
Ya yaba da yadda shugaban majalisar ke gudanar da jagoranci, wanda ke tafiya da kowa ba tare da bambancin addini ko kabila ba.
Shi ma mataimakin shugaban Karamar Hukumar Kaduna ta Kudu, Nehemiah Baba Karik, ya yaba da yadda Shugaban Majalisar yake aiki ba tare da nuna son kai ba, inda ya ce yana yi wa dukkan mazauna yankin hidima bisa adalci.
A nasa jawabin, Shugaban Majalisar Limamai da Malamai na mazabar Makera Malam Ibrahim Mahe, ya yaba da wannan karamci, inda ya ce ya zo a daidai lokacin da dace.
Ya kuma yi addu’ar Allah ya sakawa shugaban majalisar bisa kokarinsa na tallafawa al’ummar jihar Kaduna.
Wadanda suka ci gajiyar wannan karimcin sun hada da malamai maza da mata na makarantun islamiyya, da manyan limamai, da kungiyoyin Nisa’us Sunnah na Barnawa, da Makera, da Kakuri, da masu rike da sarautun gargajiya, da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC, da sauransu.
Sauran sun hada da hukumomin tsaro da suka hada da rundunar sa kai ta Civilian JTF, da kuma kungiyoyin agaji na JIBWIS, da Fityanul Islam, da Jama’atu Nasril Islam da dai sauransu.
Da dama daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin sun nuna matukar godiya ga wannan karamcin, inda suka yi addu’o’in Allah ya ci gaba da yi ma shugaban majalisar jagoranci da samun nasara a ayyukansa.
Shamsuddeen Mannir Atiku
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
