Labarai
NOA Ta Kara Daura Damarar Inganta Ayyukanta A Jihar Jigawa
Hukumar wayar da kan jama’a ta kasa, NOA, ta yi garambawul tare da wasu gyare-gyare don inganta ayyukanta a jihar Jigawa.
Daraktan riko na jihar Malam Tijjani Ibrahim ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci jami’an hukumar zuwa ziyarar ban girma ga babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar Hamisu Mohammed Gumel a gidan gwamnati na Dutse.
Ya jaddada cewa, hukumar za ta iya yin nasara ne kawai a jihar idan masu ruwa da tsaki kamar ofishin babban sakataren yada labaran suka hada hannu da ita.
Malam Tijjani Ibrahim ya ci gaba da bayanin cewa, makasudin ziyarar ita ce karfafa hadin gwiwa tsakanin NOA da ofishin sakataren, a fannin wayar da kan jama’a game da manufofi da tsare-tsare daban-daban na gwamnatin Jihar Jigawa a dukkan matakai.
A cewarsa, a shekarar 2024, NOA ta yi kokari sosai wajen wayar da kan jama’a kan katin shaidar dan kasa da kuma tsohon taken kasa da aka sake dawo da shi.
Don haka Tijjani ya jaddada cewa akwai bukatar a kara kaimi domin ganin Najeriya ta kara samun hadin kai da wadata kasa.
Da yake mayar da martani, babban sakataren yada labarai, Hamisu Mohammed Gumel ya yabawa NOA bisa wannan ziyarar.
Ya kuma yi alkawarin ci gaba da ba da goyon baya da hadin kai don cigaban bangarorin 2.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
