Connect with us

Labarai

Gwamnatin Jihar Jigawa Ta Rage Lokutan Aiki Ga Ma’aikatan Jihar

Published

on

Gwamna Umar Namadi ya rage lokutan aiki ga ma’aikatan jihar Jigawa a wannan lokaci na azumin watan Ramadan na shekarar 2025.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban ma’aikata na jihar Alhaji Muhammad K. Dagaceri ya sanyawa hannu, aka  kuma bai wa gidan rediyon Najeriya a Dutse.

Ma’aikatan jihar za su je aiki karfe 9 na safe sannan su tashi da karfe 3 na rana daga ranar Litinin zuwa Alhamis maimakon zuwa karfe 5 da ake kai wa a baya, sai ranar Juma’a ma’aikatan za su je aiki da karfe 9 na safe su tashi da karfe 1 na rana kamar yadda aka saba”.

Shugaban ma’aikatan ya bayyana cewa, an yi wannan karimci ne da nufin samarwa ma’aikatan gwamnati damammaki masu yawa na shirye-shiryen hutun watan Ramadan da kuma kara himma wajen gudanar da ayyukan ibada da ke da alaka da wannan wata mai alfarma.

Ana fatan ma’aikatan gwamnati a jihar za su yi amfani da lokacin watan Ramadan wajen yi wa jiharmu addu’a da neman albarkar Ubangiji,” in ji shugaban ma’aikatan.

Alhaji Muhammad Dagaceri ya kara jaddada bukatar ma’aikatan gwamnati su yi amfani da lokacin azumi wajen yin addu’ar zaman lafiya da ci gaban tattalin arzikin jihar da ma Najeriya baki daya.

 

Usman Muhammad Zaria

Labarai

Labarai1 hour ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi1 week ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Mafi Shahara