Labarai
Hukumar Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Ta Nemi Hadin Kan Al’ummar Jihar Jigawa
Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Jigawa ta bukaci hadin kan al’ummar jihar domin samun nasarar ayyukan da ta sanya a gaba.
Shugaban Hukumar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Jigawa (JSPCACC) Barista Salisu Abdu ya bayyana a matsayin wani muhimmin mataki na ci gaba da kokarin tabbatar da gaskiya da rikon amana a bangaren gwamnati.

Ya furta haka ne a lokacin bude taron wayar da kan jama’a na yini 3 da hukumar korafe-korafen jama’a da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Jigawa ta shirya a cibiyar bunkasa ma’aikata dake Dutse.
Ya jaddada cewa, gaskiya, da rikon amana, su ne ginshikin gudanar da shugabanci nagari.
Barista Salisu Abdu, ya kuma yi kira da a hada kai tsakanin Hukumar da hukumomin gwamnati domin yakar cin hanci da rashawa yadda ya kamata.

Gidan Rediyon Najeriya ya ruwaito cewa, taron ya hada manyan masu ruwa da tsaki, da suka hada da wakilai daga ma’aikatar shari’a, shari’a, da ICPC, da EFCC, da PCC, inda aka mayar da hankali wajen ilmantar da mahalarta taron game da aikin hukumar, da tsarin shari’a, da kuma bangarorin hadin gwiwa.
Tattaunawar ta ta’allaka ne kan ingantattun ayyuka, da hanyoyin hana almundahana da ayyukan rashawa.
Taron bitar wanda ya samu halartar manyan jami’an gwamnati, ma’aikatan gwamnati, da masu ruwa da tsaki, ya yi nuni da yadda gwamnati mai ci ke kokarin inganta shugabanci nagari da kawar da cin hanci da rashawa domin share fagen samun ci gaba mai ma’ana a jihar.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai24 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
