Connect with us

Kasuwanci

Gwamnatin Neja Ta Haramta Karbar Haraji A Hannun Masu Kananan Sana’o’i

Published

on

Gwamnatin jihar Neja ta haramta wa  masu tattara kudaden shiga a fadin kananan hukumomi ashirin da biyar na jihar karbar haraji daga hannun  ‘yan talla da masu kananan sana’o’i.

Gwamnan jihar Mohammed Umar Bago ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidan gwamnati Minna, babban birnin jihar.

Mohammed Umar Bago wanda ya yi Allah-wadai da  yadda ake karbar kudade ba bisa ka’ida ba a hannun kananan ‘yan kasuwa, ya umurci shugabannin kananan hukumomi da kansiloli da su kara sa ido tare da  tabbatar da ganin an kawo karshen irin wadannan ayyuka nan take.

Ya tunatar da su cewa gwamnatin jihar Neja tana da tsarin bai daya da ya hana karbar haraji dafa masu kananan sana’o’i domin basu  damar dogaro da kai.

Mun yanke shawarar cewa daga yanzu, babu wwanimai karamar sana’a da za a sake karbar haraji a hannunsa a wannan jihar.”

“’Yan talla da kananan ‘yan kasuwa ba sa biyan haraji a Jihar Neja,  kuma duk wanda aka samu yana karbar haraji daga wurinsu zai dandana kudarsa,” inji Gwamnan.

Daga Aliyu Lawal

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara