Labarai
An Rantsar Da Sabbin Shugabannin Kungiyar Manyan Sakatarorin Jihar Zamfara
Kungiyar manyan sakatarorin ma’aikatun jihar Zamfara(ZASPEF) ta sha alwashin ci gaba da bayar da shawarwari don inganta iyyuka da sha’anin mulki.
Zababben shugaba Malam Yakubu Sani Haidara ne ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da su a matsayin sabbin shugabannin kungiyar a Gusau.

Yakubu Sani Haidara ya bayyana cewa, yayin da ma’aikatan gwamnati ke ci gaba da bunkasa, za su ci gaba da bayar da shawarwarin ci gaba da gudanar da shirye-shirye na inganta karfin harkokin mulki.

Shugaban ya bayyana cewa, wannan yunkurin zai sa a fi amfani da shawarwarin manyan Sakatarorin wajen tsara manufofi da aiwatar da su.
Sani Haidara ya kuma ce a matsayinsu na manyan masu gudanar da mulki, ya ba da tabbacin goyon bayansu ga gwamnati mai ci ta Gwamna Dauda Lawal.

A jawabinsa na bude taron, shugaban riko na kungiyar mai barin gado Muhammad Abubakar, ya ce sun yi aiki tukuru wajen ganin sun samar da fahimtar juna a tsakanin manyan sakatarorin da ya kai ga samar da wani gagarumin dandali da ke samar da hadin kai, da bayar da shawarwari da kuma kwarewa a aiki.
Ya bukaci sabbin shugabannin da su ci gaba da inganta ayyukan yi a jihar Zamfara.

Shi ma da yake jawabi, shugaban taron kuma shugaban hukumar ma’aikatan jihar Zamfara Alhaji Aliyu Muhammad Tukur, ya yi kira ga sabbin shugabannin kungiyar da su yi aiki tukuru domin tabbatar da amincewar da aka yi musu ta hanyar sadaukar da kai da kuma aiki da gaskiya.

Sabbin shugabannin kungiyar ta Zamfara State Permanent Secretaries’ Forum (ZASPEF) sun hada da Yakubu Sani Haidara a matsayin shugaba, da Dr. Barira Ibrahim Bagobiri mataimakiyar shugaba, da Shehu Baraya Gusau a matsayin ma’ajin kudin,
da Bashir Usman Salihu jami’in hulda da jama’a.
Yayin da sauran su ne Yazid Attahiru mai binciken kudi, da
Musa Garba Bukkuyum mai bada shawara kan harkokin shari’a,
da Garba Aliyu Gayari, a matsayin Sakatare.
Aminu Dalhatu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
