Labarai
Gwamna Namadi Ya Kaddamar Da Aikin Gina Tituna Akan Kudi Naira Biliyan 6.3
Gwamna Umar Namadi ya kaddamar da aikin gina titin Kanya Babba (Kwanar Duzau) zuwa Kankare zuwa Ballada zuwa Duzau zuwa Danhill zuwa Kyambo zuwa Mundu zuwa Goron Maje.
Aikin wanda aka bayar da shi kan kudi naira biliyan 6 da miliyan 300, wani muhimmin mataki ne a yunkurin gwamnatin jihar na inganta ababen more rayuwa da hanyoyin sada yankuna.

Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Namadi ya jaddada muhimmancin hanyoyin, wajen samar da ci gaban tattalin arziki, da inganta hanyoyin samar da ababen more rayuwa, da inganta rayuwar al’ummar yankin.
Ya sake jaddada kudurin gwamnatinsa na samar da ingantattun ababen more rayuwa da za a dade ana amfana da su.

Ya kuma bayyana cewa, ana sa ran da zarar an kammala aikin zai bunkasa kasuwanci, da saukaka kalubalen sufuri, da bude sabbin hanyoyin tattalin arziki ga mazauna yankin.
Malam Umar Namadi ya ce, gwamnatin jihar ta bayar da kwangilar gina sabbin hanyoyi arba’in da bakwai na tsawon sama da kilomita dari tara a jihar.

Ya bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da ayyuka a dukkan hanyoyin da aka bayar da aikinsu.
A nasa jawabin kwamishinan ayyuka da sufuri na jihar Injiniya Gambo S Malam ya ce an bayar da aikin gina hanyar kanya Babba, zuwa Duzau zuwa Goron Maje akan kudi sama da naira biliyan shida.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, Karamar Ministar Ilimi Farfesa Suwaiba Ahmed Babura ce ta kaddamar da aikin.
Wasu daga cikin manyan baki da suka halarci bikin sun hada da, mataimakin gwamnan jihar Jigawa Injiniya Aminu Usman, da kakakin majalisar dokokin jihar Alhaji Haruna Aliyu Dangyatum da sakataren gwamnatin jihar Malam Bala Ibrahim da dai sauransu.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
