Ilimi
Gwamnatin Jihar Sakkwato Na Maraba Da Masu Zuba Jari
Gwamnatin jihar Sokoto ta ce tana kokarin samar da sauki da kuma tsarin zuba jari mai inganci wanda zai iya karfafa gwiwar masu zuba jari daga kasashen waje da na cikin gida zuwa jihar.
Wakilin Gwamnatin jiha kuma shugaban karamar hukumar Wamako Alh. Umar Ahmad Dundaye ya bayyana haka ne a wajen rabon magunguna da kamfanin siminti na BUA ke gabatarwa a kowace shekara ga asibitocin al’umma goma sha shida da ke yankin.
Ya ce gwamnatin jihar Sokoto tana karfafa duk masu zuba jari da ke da alaka kai tsaye ga ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin jihar.
Ya ce gudunmawar BUA a fannin kiwon lafiya na jihar na daya daga cikin alfanun da jarin jihar ke samu.
Shugaban ya kara da cewa, a wani bangare na ayyukan da ya rataya a wuyan kamfanin, kamfanin yana kara habaka dimbin albarkatu wajen bunkasa al’ummomin da suka karbi bakuncinsa a karkashin karamar hukumar Wamako.
A nasa jawabin, Manajan Daraktan kamfanin simintin Alh. Yusuf Binji ya ce tallafawa al’ummomin da suka karbi bakuncinsu yana da matukar muhimmanci a wani yunkuri na kara kima ga zamantakewa da zaman lafiya da ci gaban tattalin arzikin jama’ar yankin.
Nasir Malali/Wababe
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai2 days ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai4 hours agoAKCILS Ta Karrama Jami’in Tsaro Bayan Shekaru 22
-
Labarai2 days ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
