Labarai
Gwamnatin Jigawa Za Ta Kara Habbaka Noman Dabino A Jihar
Gwamnatin Jihar Jigawa ta kara jaddada kudurinta na yin hadin gwiwa da wani kamfanin sarrafa dabino da kayan marmari domin inganta noman dabino da alkama a jihar.

Gwamna Umar Namadi ya bada wannan tabbaci a lokacin da tawagar Babban Daraktan kamfanin, Dakta Abubakar Musa Bamai ta ziyarci shi a gidan Gwamnati dake Dutse, Babban Birnin Jihar.

Ya bayyana cewar, Gwamnatin a shirye take ta yi aiki tare da kowace kungiya da ke da niyyar tallafa wa jin daɗin al’umma da ci gaban tattalin arzikin jihar jigawa.

Malam Umar Namadi ya kara da cewar a zancen ma dai da ake yi a halin yanzu, Jihar Jigawa ta shahara wajen noman dabino kuma ita ce ta daya a noman alkama a ƙasar nan.

Kazalika, yayi nuni da cewar ana shirin amfani da fasahar zamani domin habaka harkar noma don ci gaba da riƙe wannan matsayi.

Tunda farko a jawabinsa, Babban Daraktan kamfanin, Dakta Abubakar Musa Bamai, ya bayyana cewar sun kai ziyarar ce domin tattauna hanyoyin hadin gwiwa da Gwamnatin Jihar Jigawa wajen kafa gonakin dabino da inganta noman alkama ta amfani da fasahar zamani.

Namadi, ya ce gonakin za su kunshi nau’uka hudu na dabino da za su bai wa jihar damar fara fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje maimakon amfani da su a cikin gida kawai.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
