Connect with us

Labarai

Kungiyar Nawoj Reshen Kano Na Neman Goyon Bayan Gwamnati

Published

on

Kungiyar mata ‘yan jarida ta Najeriya (NAWOJ) reshen jihar Kano, ta yi alkawarin hada kai da gwamnatin jihar Kano domin horar da mambobinta da taimakawa wajen yada bayanai kan ayyukan gwamnati.

 

An yi wannan alkawari ne a wata ziyarar fahimtar da NAWOJ ta kai wa sabon kwamishinan yada labarai na jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya.

 

Shugabar kungiyar ta NAWOJ reshen Kano, Kwamared Bahijja Kabara, ta yabawa kwamishinan bisa jajircewarsa na inganta ayyukan mata ‘yan jarida ta hanyar horas da su.

 

Ta kuma jaddada cewa irin wannan kokarin zai inganta kwarewa da ingancin aikin jarida a jihar.

 

Kwamishinan yada labarai, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya nuna jin dadinsa ga NAWOJ bisa ziyarar da suka kai tare da bada tabbacin kungiyar na ci gaba da marawa gwamnati baya.

 

Ya amince da muhimmiyar rawar da mata ‘yan jarida ke takawa wajen yada labarai kuma ya yi alkawarin ba da fifikon karfafa su ta hanyar horar da su da kuma shirye-shirye masu inganci.

 

Sakatariyar kungiyar NAWOJ ta kasa, Kwamared Wasila Ibrahim Aladan, ta bayyana mahimmancin hadin kai tsakanin kafafen yada labarai da gwamnati wajen tabbatar da ingantaccen sadarwa da wayar da kan jama’a.

 

A nata jawabai Hajiya Salma Yusuf wadda ta nuna godiya ga Gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa goyon bayan da yake bai wa mata, inda ta bayyana shi a matsayin mai fafutukar karfafa gwiwar mata.

 

Ta kuma yabawa Kwamared Waiya bisa yadda yake samar da tsare-tsare masu dacewa da kafafen yada labarai da inganta hadin gwiwa da masu ruwa da tsaki.

 

Wannan ziyarar ta nuna jajircewar NAWOJ wajen ciyar da aikin jarida gaba, karfafawa mata gwiwa, da tallafawa shirye-shiryen gwamnati da ke da nufin ci gaban al’umma.

 

KHADIJAH ALIYU/Wababe

Labarai

Labarai21 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai24 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara