Labarai
Jahar Kwara ta gudanar da gwajin Hawan jini, sukari ga Mutane dubu 102 Kauta
Ma’aikatar lafiya ta jihar Kwara ta ce ta yi wa sama da mutane dubu dari da biyu (102,452) gwajin cutar hawan jini da ciwon suga a fadin kananan hukumomin jihar 16 daga watan Oktoba zuwa Disambar bara.
Kwamishiniyar lafiya ta jihar, Dakta Amina El-Imam, ta bayyana hakan a lokacin da take zantawa da manema labarai akan ayyukan ma’aikatar a Ilorin.
Ta ce an kuma ba da magungunan kyauta ga duk mutanen da aka sani da cutar hawan jini da ciwon sukari a lokacin motsa jiki.
Kwamishinar taa ce an sake horar da ma’aikatan kiwon lafiya a wuraren kiwon lafiya na matakin farko dana mataki na biyu da kuma manyan cibiyoyin lafiya game da wannan cuta.
Dakta El-Imam ta kuma ce an gudanar da aikin tantance cutar sankarar mama da mahaifa kyauta a fadin kananan hukumomi 16 na jihar a tsawon wannan lokaci.
Ta yi bayanin cewa an yi wa mata 1,151 da 807 gwajin cutar kansar nono da mahaifa, inda ta kara da cewa duk wadanda suka kamu da cutar suna karkashin kulawa a asibitin koyarwa na jami’ar jihar (KWASUTH).
Kwamishinan ta lura cewa inganta kula da masu fama da tarin fuka ya haifar da nasarar samun maganin kashi 94 cikin 100 a shekarar data gabata ta 2024.
Ta ci gaba da cewa, an gudanar da ayyukan ba da magunguna kyauta a kan yara sama da 750,000 a makaranta da makarantun gwamnati da masu zaman kansu da kuma al’ummomi a fadin jihar.
COV/ALI MUHAMMAD RABIU
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
