Connect with us

Labarai

Iyalan Olatunji Jimoh sun koka kan mutuwarsa a hannun ‘yan sanda

Published

on

An yi kira ga rundunar ‘yan sandan Najeriya da ta gaggauta gudanar da bincike kan zargin azabtarwa da kuma kashe wani manomi mai suna Olatunji Jimoh mai shekaru 35 a hannun ‘yan sanda a garin Ilorin na jihar Kwara.

 

Da yake jawabi ga manema labarai kan lamarin a Ilorin a madadin iyalan Jimoh Alabi, wani dan kasa kuma mai gabatar da kara, Owolabi Olumuyiwa, ya ce marigayin na hannun ‘yan sanda ne bisa bashi.

A cewarsa a ranar 19 ga watan Disambar bara, wani kehinde Jelili ne ya yaudare marigayin a lokacin da yake wanke tufafi a gidansa da ke unguwar Balogun Fulani a Ilorin. Ya ce jami’an hukumar bincike na musamman na ‘yan sandan Najeriya (SIB) ne suka yi awon gaba da Olatunji a kan babur suka ajiye shi a hedikwatar ‘yan sanda da ke Ilorin.

 

Olumuyiwa ya bayyana cewa da misalin karfe shida na yammacin wannan rana marigayin ya yi waya da ‘yan uwansa wadanda daga baya suka zo hedikwatar ‘yan sanda domin shaida cewa shi (Olatunji) marigayin yana bin babban sa Gabriel Sunday kudi naira dubu dari da ashirin .

 

Ya kara da cewa ko a lokacin da iyalan suka biya kudin daga cikin jimillar Naira dubu 425 da aka gano ga mamacin, jami’an ‘yan sanda Adekunle Emmanuel Ogunsola, Emmanuel Ajiboye, da Oluwole Bamiteko sun hana su belinsa, inda suka umurci iyalin da su dawo washegari da safe.

 

Olumuyiwa ya ce da misalin karfe goma na dare wani bakon waya da aka yi wa ‘yar uwar marigayiyar ana neman su zo ofishin, ya kara da cewa marigayin ya rataye kansa a caji ofis na ‘yan sanda kuma ya mutu. Ya yi nuni da cewa a lokacin da ‘yan uwa suka bukaci a mika musu gawar marigayin (Olatunji) ‘yan sanda sun ce an kai gawar dakin ajiyar gawa tare da yayyaga masa cinyarsa, tare da raunuka a jikinsa ba tare da amincewar dangin ba.

 

Olumuyiwa ya roki babban sufeton ‘yan sanda da ya ba da umarnin gudanar da bincike don gano musabbabin mutuwar Olatunji. Ya ce jami’an ‘yan sandan da suka kama shi ba bisa ka’ida ba, a gurfanar da su a gaban kuliya, sannan a duba lafiyar ‘ya’yansa biyu.

 

A nasu jawabin mahaifin marigayin, Jimoh Alabi da mahaifiyar Adijat Jimoh sun kuma bukaci hukumar ‘yan sandan da ta biya su diyya sakamakon kaduwa da suka yi na mutuwar dan nasu.

 

A nasa bangaren, Lauyan iyalan Olatunji, Barista Olukayode Oloyede ya roki babban sufeton ‘yan sandan da ya binciki al’amuran da suka shafi wuce gona da iri a jihar Kwara da nufin kawo karshen kashe-kashen da ake yi wa ‘yan kasa da ba su ji ba ba su gani ba.

COV/ALI MUHAMMAD RABIU/Wababe

Labarai

Labarai1 hour ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi1 week ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Mafi Shahara