Ilimi
WAEC Ta Sanar Da Sabon Tsarin Rubuta Jarabawa Ga Dalibai
Hukumar Shirya Jarabawar Kammala Sakandare Ta Afirka Ta Yamma WAEC, Ta fitar da sabon tsarin da zai bai wa dalibai damar sake zama rubuta jarabawa daga watan Janairu zuwa Faburairu na wannan shekara.
Shugaban sashin hulda da jama’a na hukumar Mr John Kapi, ya fadi hakan a cikin wani shiri na talabijin Ghana, inda ya ce wannan tsarin wani gagarumin sauyi ne daga tsarin da ake yi a baya, inda sai dai dalibai su jira wani zagayen kafin su sake rajistar rubuta jarabawar.
Mr John Kapi ya yi bayanin cewa, wannan sabon tsarin zai samar wa dalibai damar bunkasa kwazonsu, sannan daliban da suka san cewa za su sake rubuta jarabawar, to suna da damar nan da ranar 8 ga watan Janairu domin yin rajistar ta WAEC a cibiyoyin da hukumar ta amince da su.
Ya ce su ma daliban da aka soke jarabawarsu, za su iya rubuta wannan jarabawar, muddin ba a dakatar da su daga rubuta jarabawar ba na wasu shekaru saboda aikata magudi.
RN
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai24 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
