Labarai
Shugaba Tinubu Zai Tafi Ghana Bikin Rantsar Da Sabon Shugaban Kasa
Yau shugaba Bola Tinubu zai tashi daga Abuja zuwa Accra babban birnin jamhuriyar Ghana domin halartar bikin rantsar da zababben shugaban kasar John Dramani Mahama a ranar 7 ga watan Janairu.
Mahama, wanda ya zama shugaban kasar Ghana na 12 tsakanin shekarar 2011 zuwa 2017, an sake zabensa ne a watan Disambar 2024.
Zai gaji shugaba Nana Akufo-Addo, wanda ya yi mulki tsakanin 2017 zuwa 2025.
Sanarwar ta ce tafiyar Shugaba Tinubu zuwa Accra na zuwa ne bisa gayyatar zababben shugaban kasar, wanda ya kai masa ziyara a Abuja a farkon watan Disamba.
Sanarwar mai dauke da sa hannun mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Mista Bayo Onanuga, ta ce Mahama da shugaba Tinubu na da dadaddiyar alaka, kamar yadda Najeriya da Ghana ke da dadadden alaka tsakanin kasashen biyu.
Ta ce shugaba Tinubu, a matsayinsa na shugaban kungiyar ECOWAS, zai bi sahun sauran shugabannin kasashen Afrika wajen bikin.
Ya bayyana cewa Ministar Kasa a Ma’aikatar Harkokin Waje, Misis Bianca Odumegwu-Ojukwu da wasu manyan jami’an gwamnati za su raka shugaba Tinubu a wannan tafiya.
Bello Wakili/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
