Labarai
Rundunar Samamen Fansar Yamma Na Samun Nasarori ‘Yan Kwanakin Nan
Dakarun rundunar hadin gwiwa dake aiki a Arewa maso Yamma, samamen Fansan Yamma sun gudanar da sintiri a kauyen Bamamu da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara inda suka yi arangama da ‘yan ta’addan a yankin tare da kashe wani dan ta’addan da ya shahara Sani Rusu.
Babban jami’in yada labaran Rundunar Fansan Yamma, Laftanar Kanar, Abubukar Abdullahi ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya ba rediyon Najeriya dake Gusau.
Sanarwar ta ce, a wannan rana, sojojin na Samamen Fansan Yamma, a yayin wani samame na kwanton bauna da aka yi bisa sahihan bayanan sirri dangane da ayyukan ta’addanci a Kwanar Jollof da ke karamar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara, sun kashe wasu ‘yan ta’addan, yayin da wasu kuma suka samu munanan raunuka.
Sanarwar ta bayyana cewa, a wani samame na daban, rundunar sojin sama ta Operation Fansan Yamma ta kai farmaki ta sama kan ‘yan ta’addan da ke taruwa a tsakanin Fakai da yankin Kware na karamar hukumar Shinkafi a ranar 30 ga watan Disamba 2024.
An kaddamar da harin ta sama ne a matsayin martani ga bayanan sirri da aka samu cewa ‘yan ta’addan karkashin jagorancin Bello Turji sun gudanar da taro a yankin.
Sanarwar ta kuma bayyana cewa, sojojin sun kuma kai farmaki a sansanin Bello Turji da ke yankin Chida a Shinkafi a ranar 5 ga watan Janairun 2025.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, Operation Fansan Yamma na ci gaba da jajircewa wajen kawar da duk wata barazana ta ‘yan ta’adda a duk fadin yankin don tabbatar wa al’umma aniyar ta na wanzar da zaman lafiya da tsaro a yankin.
REL/AMINU DALHATU/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
