Labarai
Hamas ta saki sunayen da za ta saki a yarjejeniyar kawo Karshen yaki
Wani babban jami’in Hamas ya bayyanawa BBC jerin sunayen mutane 34 da kungiyar Falasdinawan ta yi garkuwa da su wanda ta shirya sakowa a matakin farko na yarjejeniyar tsagaita wuta da a iya cimma da Isra’ila.
Ba a tabbatar da adadin mutanen da aka yi garkuwa da su da ke raye ba a halin da ake ciki yanzu.
Daga cikin wadanda aka bayyana sunayensu akwai mata 10 da kuma maza 11 masu shekaru tsakanin 50 zuwa 85, da kuma kananan yara da a baya Hamas ta yi ikirarin cewa sun mutu a wani harin da Isra’ila ta kai.
Jerin sunayen dai, ya kuma kunshi mutanen da Hamas din ta ce na fama da rashin lafiya.
Sai dai ofishin Firaministan Isra’ilar ya musanta wasu rahotanni da ke cewa kungiyar ta baiwa kasar wadannan sunaye.
A karshen mako ne aka dawo da tattaunawar tsagaita wuta tsakanin bangarorin biyu, a birnin Doha na kasar Qatar, sai dai da alama ba a samu wani gagarumin ci gaba ba tukunna.
Wani jami’in Hamas ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa duk wata yarjejeniya ta mayar da mutanen Isra’ila da aka yi garkuwa da su za ta dogara ne kan amincewar kasarsu, ta fice daga zirin Gaza, kana ta kawo karshen yakin baki daya.
Sai dai a cewarsa, har kawo yanzu babu wani yunkuri da Isra’ilar ta yi na nuna da gaske take.
Tun da farko dai, Hamas ta saki bidiyon wata fursuna yar shekaru 19, Liri Albag, inda ta yi kira ga gwamnatin kasar ta kulla yarjejeniya da Hamas.
Rahotanni daga Gaza, na cewa a iya karshen makon nan kadai, hare-haren da Isra’ila ta kai ta sama sun kashe mutane fiye da 100.
Wata majiya ta ce hare-haren sun kashe mutane 88 a shekaran-jiya Asabar kadai, yayin da a jiya Lahadin kuma, majiyoyin lafiya suka ce karin wasu 17 sun mutu a wasu hare-haren na daban.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
