Labarai
Gwamna Namadi Ya Nada Masu Bashi Shawara Na Musamman Su 5
Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya amince da nadin karin masu ba da shawara na musamman guda 5.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jiha Malam Bala Ibrahim ya sanyawa hannu kuma ya mikawa manema labarai a Dutse.
Ya ce, wadanda aka nada sun hada da Abdulkadir Bala Umar T.O mai ba da shawara na musamman kan ayyuka na musamman, Uzairu Nadabo mai ba da shawara na musamman 2 EPZ da Ado Mai’unguwa mai ba da shawara na musamman kan kasuwanci.
Musa Shu’aibu Guri a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkokin kudaden shiga yayin da Sa’idu Umar ya samu matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkokin abinci.
Malam Bala Ibrahim ya bayyana cewa, anyi wannan nadin ne bias cancanta da cancanta.
“A yayin da nake taya sabbin mukaman da aka nada, ina kira gare ku da ku kasance masu gaskiya da adalci wajen sauke nauyin da aka dora muku, muna da babban aiki a gaban ku, kuma dukkan ku dole ne ku lura tare da aiki daidai da ajandar 12 na Gwamna Umar Namadi, domin gina jihar Jigawa.” in ji sakataren gwamnatin.
Bala Ibrahim ya kara da cewa, duk nade-naden ya fara aiki nan take.
KARSHE/USMAN MZ/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
