Kasuwanci
Za a Tabbatar Adalci Wajen Rabon Kayan Tallafin Ramadan na AA Yari a Zamfara
Kwamitin rabon tallafin watan Ramadan na tsohon gwamnan jihar Zamfara, Dr Abdul’azeez Yari Abubakar ya ce an tsara shirye-shirye domin samun nasarar rabon kayan tallafin watan Ramadan na bana.
Shugaban kwamatin rabon kayayyaki Alhaji Lawal M. Liman ya bayyana haka bayan kammala taron kwamitin da Sanata Abdulaziz Yari Abubakar a gidansa dakeTalata Mafara a jihar Zamfara.
Ya ce makasudin taron shi ne gyara ayyukan kwamitin a kokarinsa na ganin ya dauki nauyin da ya rataya a wuyansa.
A cewar Alhaji Liman, a yayin taron, mambobin kwamitin sun yi bitar aikin da aka yi a baya yayin da aka tattauna nasarori da kalubale.
Ya jaddada cewa, an tsara jadawali kafin a fara gudanar da aikin bada tallafin na watan Ramadan na bana domin a samu sauki.
A wata sanarwa da shugaban kwamitin yada labarai na kungiyar siyasa A A Yari, Alhaji Ibrahim Muhammad ya fitar, Danmadamin Birnin Magajii ya ce wanda ya kaddamar da shirin kuma Sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta yamma, Alhaji Abdulaziz Yari Abubakar ya bayyana fatansa na ganin an gudanar da gaskiya da adalci wajen wannan rabon.
REL/AMINU DALHATU/Wababe
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
