Kasuwanci
Ma’aikata Sun Koma Bakin Aiki Bayan Kammala Hutun Kirsemeti
Ma’aikatan gwamnati a Kano sun ci gaba da gudanar da ayyukansu a daidai lokacin da ake kawo karshen bukukuwan Kirsimeti.
Ziyarar da aka kai a Sakatariyar Gwamnatin Tarayya da ke kan titin Katsina, Kano, ta nuna cewa ma’aikatan gwamnati sun koma bakin aiki gaba daya.
Hatta wadanda suka yi tafiya hutu an ga sun dawo bakin aiki.
Hakazalika, a sakatariyar gwamnatin jihar Kano ta Audu Bako, an ci gaba da gudanar da ayyuka cikin sauri.
Baya ga sake dawo da ma’aikatan gwamnati, har ila yau harkokin kasuwanci a manyan kasuwannin Kano sun ci gaba.
Ziyarar da aka kai kasuwannin ta nuna cewa ’yan kasuwa daga sassa daban-daban na kasar nan suna ta tururuwa zuwa cibiyar kasuwancin Arewa don gudanar da kasuwanci.
Sabbin al’amura a kasuwanni da ma’aikatun gwamnati na nuni da cewa rayuwa ta koma daidai a Kano bayan bukukuwan Kirsimeti.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO/Wababe
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
