Connect with us

Labarai

Mahukunta Gidan Rediyon Tarayyar Najeriya Sun Kai Ziyarar Ta’aziyya Jihar Jigawa

Published

on

Darakta Janar na Gidan Rediyon Tarayyar Najeriya FRCN, Dr Mohammed Bulama ya mika ta’aziyya ga Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa bisa rasuwar mahaifiyarsa da babban dansa.

Shugaban ya bayyana  jimaminsa game da wannan babban rashi, inda ya bayyana shi a matsayin abi mai matukar raɗaɗi.

Dokta Mohammed Bulama wanda ya jagoranci wasu ma’aikatan hukumar zuwa gidan gwamnati da ke Dutse babban birnin jihar ta Jigawa, ya bukaci Gwamnan da ya mika lamuransa.

Lalle irin wannan rashi na da radadi matuka,  amma muna kara tunasar da kanmu a kullum cewa rayuwa da mutuwa suna hannun Allah SWT kuma dukkanmu muna jiran lokaci ne”.

Bulama ya yi addu’ar Allah Ya bai wa Gwamnan da iyalansa da daukacin al’ummar jihar Jigawa ikon jure wannan rashi maras misaltuwa.

Da yake mayar da martani, Gwamna Umar Namadi ya godewa hukumar ta Rediyon Tarayyar Najeriya  bisa wannan ziyarar ta’aziyyar.

Namadi ya ce, hakan na nuni da  alamar kyakyawar alakar da ke tsakanin gidan rediyon da gwamnatin jihar.

Ya ce, rasuwar mahaifiyarsa da dansa jarrabawa ce daga Allah, inda ya ce a matsayinsa na musulmi yana da yakinin cewa dukkan mai rai mamaci ne.

 

Usman Muhammad Zaria

Labarai

Labarai2 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi1 week ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Mafi Shahara