Labarai
Kudirin Kasafin Kudi Na Shekarar 2025 A Jihar Jigawa Ya Samu Amincewar Majalisar Dokokin Jihar
Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta amince da kudurin kasafin kudin shekara ta 2025 na sama da naira miliyan dubu 698.
Haka kuma majalissar ta amince da kasafin kudin kananan hukumomin jihar 27, na naira miliyan dubu 184 da miliyan 491.
Daukar wannan mataki ya biyo bayan gabatarwa da kuma amincewa da rahoton kwamatin kasafin kudi na majalisar ya yi.
Da ya ke gabatar da rahotonsa, shugaban kwamitin kuma wakilin mazabar Malam Madori Alhaji Hamza Hamza Adamu Ibrahim, ya ce dukkan kwamitocin Majalisar sun tantance kiyasin kasafin kudaden ma’aikatu da hukumomin gwamnatin jihar, domin samar da karin kudade ko kuma daidaito kan abubuwan da ke kunshe cikin kasafin kudin.
A cewar sa, baya da ganawa da masu ruwa da tsaki kwamitocin sun ji ta bakin kungiyoyin kyautata jin dadin al’umma daban daban, tare da zama na musamman da dukkan kwamitocin Majalisar a lokaci daya, domin gudanar da gyare gyare da cimma matsaya dan samar da cikakken daftarin kasafin kudi da kwamatin zai mikawa majalisar kamar yadda aka dora masa nauyin wannan aiki.
Bayan samun goyon baya da gagarumin rinjaye sai shugaban majalisar dokokin jihar Jigawa, Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin ya sanar da amincewa da kudurin kiyasin kasafin kudin na sabuwar shekara ta 2025 ya zamo doka.
Usman Mohammed Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
