Connect with us

Labarai

Karamar Hukumar Kauru Ta Raba Kayayyakin Abinci Na Miliyoyin Naira Ga Marasa Galihu

Published

on

A kokarin da take na inganta rayuwar al’umma, Majalisar Karamar Hukumar Kauru da ke Jihar Kaduna ta raba kayayyakin abinci na  miliyoyin Naira ga marasa galihu.

A cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na majalisar Alhaji Sani Yahaya ya fitar, ya ce an shirya wannan karamcin ne da nufin rage matsalolin tattalin arziki da mazauna yankin ke fuskanta sakamakon cire tallafin man fetur da aka yi a baya-bayan nan, wanda ya haifar da tashin gwauron zabin farashin kayayyakin abinci.

Shugaban karamar hukumar Alhaji Bashir Tanko Dawaki ne ya kaddamar da rabon kayayyakin a hukumance a Kauru.

Ya bayyana cewa an zabo wadanda suka ci gajiyar shirin ne daga sassan kananan hukumomin domin tabbatar da ganin wadanda suka cancanta ne suka amfana, tare da yin rabon bisa adalci.

Alhaji Bashir Tanko Dawaki ya bukaci masu ruwa da tsaki wajen rabon kayan abinci da su tabbatar da adalci, don ganin tallafin ya isa ga wadanda suka cancanta a gundumomi  goma sha daya da ke yankin.

Ya kuma yabawa gwamnatin jihar karkashin jagorancin Gwamna Uba Sani, bisa kokarin da ta yi wajen bullo da shirye-shirye da ayyukan da ke da tasiri ga rayuwar aal’umma.

Shugaban ya shawarci wadanda suka ci gajiyar tallafin da su yi amfani da kayan abinci yadda ya kamata, ya kuma yi kira ga wadanda ba su samu ba a wannan karon da su yi hakuri, domin za a  kara wani rabon nan gaba kadan.

Wadanda suka ci gajiyar shirin sun nuna jin dadinsu ga majalisar karamar hukumar bisa wannan karamci.

Sun yi alkawarin bayar da goyon bayansu ga gwamnati mai ci, tare da yi mata addu’ar samun nasara.

An raba buhunan abinci daban daban guda 886 da suka hada da masara, gero, da dawa, inda aka bada fifiko ga mata da masu rauni a cikin al’umma.

Wannan kokarin da karamar hukumar Kauru ta yi ya jaddada kudirinta na tallafa wa marasa galihu domin rage radadin matsin rayuwa da ya addabi al’umma.

 

Yusuf Zubairu

Labarai

Labarai6 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai9 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai7 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai7 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai7 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai7 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai7 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara