Labarai
Babu Katsalanda A Ayukkan Majalisar Jihar Jigawa – Shugaba
Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Jigawa Alhaji Haruna Aliyu Dangyatin ya ce gwamnatin Gwamna Umar Namadi ba ta tsoma baki a harkokin majalisa tun farkon kama mulki.
Shugaban majalisar wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake tsokaci kan cika shekara guda a kan karagar mulki Gwamna Malam Umar Namadi a wata tattaunawa da manema labarai a Dutse inda ya ce gwamnati ta kawo wa al’umma ci gaban da ba a taba ganin irinsa ba a cikin wannan shekarar.
Haruna Aliyu Dangyatin ya bayyana cewa gwamnati ta dauki matasa dubu 6,368 aiki a matsayin malamai da ma’aikatan lafiya yayin da gwamnan ya bayar da umarnin kwashe matasa 1,500 a karkashin shirin kula da Lafiya da na aikin gona kowanne da karin matasa 3000 a karkashin shirin fasahar zamana. .
A cewarsa, a kwanakin baya ne majalisar ta zartar da dokokin kafa hukumomi takwas da suka hada da babbar hukumar kula da harkokin ilimi ta kasa da kasa, hukumar fasahar bayanai da tattalin arziki ta jihar Jigawa, hukumar Hizba, hukumar kula da makarantun Tsangaya da dai sauransu domin ci gaban jihar.
Ya yi nuni da cewa, gwamnatin Gwamna Umar Namadi ta nuna himma wajen noman alkama wanda zai kai ga samun girbi mai yawa.
KARSHE/USMAN MZ/Khalifa/Abdurrahman/Wababe
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai24 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
