Labarai
Gwamnatin Jigawa Ta Kaddamar Da Harsashin Ginin Dindindin Na Kwalejin Jinya Ta Hadejia
Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya kaddamar da bikin aza harsashin gina rukunin dindindin na kwalejin jinya da ungozoma da ke Hadejia na naira biliyan biyar da rabi domin samar da isassun ma’aikata da kwararru a fannin lafiya.
Gwamnan ya bayyana cewa ingantaccen tsarin kiwon lafiya wani muhimmin alkawari ne da aka yi gabanin zabe wanda aka sanya shi cikin tsare-tsare guda 12 don ci gaban jihar Jigawa baki daya.

Ya ce aikin wanda ya kasu kashi biyu, ana sa ran kammala shi a cikin watanni 18 inda za a kashe naira biliyan 3 da kuma Naira biliyan 2 da rabi bi da bi.
Mallam Umar Namadi ya ci gaba da cewa, gwamnatin sa ta kuma yi niyyar samar da babban asibiti a kowace mazabar majalisar jiha 30 da kuma cibiyar kula da lafiya a matakin farko a kowace gunduma.

Ya ce, wannan kari ne ga asibitocin kwararru da aka kafa a shiyyoyi t3 na jihar.
Namadi ya kuma ce, domin tabbatar da isassun ma’aikatan lafiya, gwamnati ta tura sama da dalibai 109 zuwa kasar Cyprus don yin karatun likitanci, tare da karin karatu a cikin gida.
Ya yi nuni da cewa, akwai kwalejojin aikin jinya da ungozoma guda uku a Birninkudu, Babura, da Hadejia, Gwamnan ya ce yana da kwarin guiwar samun ma’aikatan lafiya kwararru.
Usman Muhammad Zaria
-
Labarai4 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai5 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai5 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai5 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai4 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai3 days agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai2 days agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
-
Labarai3 days agoShugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus
