Connect with us

Labarai

Wani Fasinja Ya Yi Kashin Sama Da Dauri 100 Na Hodar Ibilis- NDLEA

Published

on

Hukumar yaki da safarar miyagun kwayoyi a Najeriya NDLEA ta ce yanzu haka ta na rike da wani fasinjan jirgin saman dake kan hanyar zuwa birnin Paris ta kasar Faransa saboda zargin mallakar hodar ibilis,  inda ya yi  kashin dauri dari daya da goma sha daya na hodar da ya hadiye a cikinsa bayan an kama shi.

Mai magana da yawun hukumar Femi Babafemi yace sun kama wannan mutumin mai suna Emmanuel Okechukwu Orjinze ne a tashar jiragen saman Abuja lokacin da yake kokarin tsallake wuraren binciken fasinjoji domin hawa jirgin sama.

Okechukwu ya shaidawa NDLEA cewar shi ‘dan kwallo ne a Turai lokacin da aka kama shi a ranar 21 ga wannan wata a daidai lokacin da yake kokarin hawa jirgin Air France mai lamba 878 dake shirin barin Abuja zuwa Paris.

Wanda ake zargi, Emmanuel Okechukwu Orjinze
Emmanuel Okechukwu Orjinze

Bayan gudanar da bincike a kansa da na’ura, an tabbatar da cewar akwai tarin kunshin hodar ibilis wato cocaine a cikin sa, abin da ya sa aka tsare shi na tsawon kwanaki 3 kuma aka yi sa’ar ganin ya yi kashin wadannan dauri 111 da nauyin su ya kai kilo  1,603.

Yanzu dai haka Okechukwu na can a tsare inda ake sa ran gabatar da shi a gaban kotu domin amsa tambayoyin hukumomin shari’a.

Babafemi ya kuma bayyana nasarar da hukumar NDLEA ta samu na tarwatsa wata kungiya ta masu hadahadar  miyagun kwayoyi a tashar jiragen saman Lagos, tare da kama mutane 4  daga cikin su da kuma kwace kilo 8 na hodar methamphetamine da kilo 7 da rabi na kwayar da ake kira cloud da ake safarar ta daga kasar Afirka ta kudu.

Jami’in yace ya yin gudanar da bincike, an kuma kama wasu karin mutane 2 a unguwar rukunin gidajen dake Ajao Estate dake birnin na Lagos.

Labarai

Labarai21 hours ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai24 hours ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara