Labarai
Jigawa Za Ta Samar Da Kimanin Kashi 30 Na Shinkafar Da Najeriya Ke Bukata
Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya ce gwamnatinsa ta yi nasarar tallafa wa manoma don noma sama da hekta 200,000 na shinkafa a bana, inda ake sa ran girbar sama da tan 800,000.
Ya bayyana haka ne a lokacin da ya duba wasu gonakin shinkafa da ke rafin Hadejia a kananan hukumomin Ringim, Taura, Auyo da Hadejia.

A cewarsa, noma na daya daga cikin muhimmin bangare na manufofinsa guda 12, domin kawar da fatara, da samar da ayyukan yi, da wadata kasa da abinci, da kuma ci gaban tattalin arziki mai dorewa.
Mallam Umar Namadi ya bayyana cewa, an tallafawa manoman da kayan amfanin gona iri-iri a farashi mai rahusa, da kuma rance mai sauki wanda ya ba su damar noma mai dimbin yawa.
Ya yi nuni da cewa, ana sa ran samar da tan 800,000 a wannan lokaci na rani, da kuma kwatankwacin hakan a daminar bana.

Ya yi nuni da cewa, jihar za ta samar da tan miliyan daya da dubu dari takwas wanda yayi daidai da kashi 27 bisa dari na shinkafar da ake bukata a duk shekara a Najeriya.
Umar Namadi ya shaida wa manoman cewa, gwamnatinsa na sane da yanayin tsadar man fetur, wanda ke kawo cikas wajen samar da isasshen ruwa yayin nomar rani, inda ya yi alkawarin hada hannu da gwamnatin tarayya domin samar musu da tallafi.

Ya kuma yi alkawarin samar da ruwan famfo mai amfani da hasken rana akan farashi mai rahusa ga manoma domin saukaka ayyukansu.
Gwamnan ya yabawa manoman bisa yadda suka nuna jajircewarsu wajen gudanar da sana’arsu, wanda ya bayyana a matsayin abin alfahari.

Da yake jawabi a madadin manoman, Alhaji Dauda Ali Kura ya bayyana cewa, babbar matsalarsu a noman rani ita ce tsadar man fetur, domin shi kadai yana kashe sama da naira miliyan 1 wajen sayen mai a duk mako.
Kura ya yi kira ga Gwamnan da ya kara samar masu da hanyoyin da za su ci gaba da yin noma.
Usman Muhammad Zaria
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai6 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai4 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
