Labarai
Gwamnatin Kwara Ta Bada Tallafin Kayan Aikin Gona Ga Manoman Shinkafa
Akalla kungiyoyin manoman shinkafa talatin ne a karamar hukumar Edu ta jihar Kwara suka ci gajiyar shirin rabon kayan amfanin gona na gwamnatinjihar.
Kwamishinar noma da raya karkara ta jihar, Misis Oloruntoyosi Thomas ta bayyana haka a lokacin da take kula da rabon kayan amfanin gona ga kungiyoyi manoma a kauyukan Yelwa, da Bacita.
Ta yabawa Gwamnan jihar bisa namijin kokarin da ya yi na ganin an samu wadatar abinci a jihar.

Misis Thomas ta bayyana farin cikinta kan yadda aka samu nasarar rarraba kayayyakin a yankin.
Kwamishinar ta shawarci manoman da suka amfana da su tabbatar da yin amfani da kayan aikin gonan yadda ya kamata.
A nasa jawabin a madadin wadanda suka ci gajiyar tallafin, Shugaban kungiyar manoma ta Najeriya (AFAN) reshen jihar Kwara, Umar Mahmud-Aboki ya yabawa gwamnatin jihar kan yadda ta kai dauki ga manoma.
Tun da farko a nasa jawabin Etsu Tsaragi, Alhaji Aliyu Abdullahi wanda Santuraki na Tsaragi ya wakilta, Alhaji Jubril Gana -Jubril ya godewa gwamnatin jihar bisa aiwatar da shirin inganta rayuwar manoma.
Ali Muhammad Rabi’u
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai20 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai22 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
