Connect with us

Labarai

Jigawa Za Ta Samar Da Kimanin Kashi 30 Na Shinkafar Da Najeriya Ke Bukata

Published

on

Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa ya ce gwamnatinsa ta yi nasarar tallafa wa manoma don noma sama da hekta 200,000 na shinkafa a bana, inda ake sa  ran  girbar sama da tan 800,000.

Ya bayyana haka ne a lokacin da ya duba wasu gonakin shinkafa da ke rafin Hadejia a kananan hukumomin Ringim, Taura, Auyo da Hadejia.

A cewarsa, noma na daya daga cikin muhimmin bangare na manufofinsa guda 12, domin kawar da fatara, da  samar da ayyukan yi, da wadata kasa da  abinci, da kuma ci gaban tattalin arziki mai dorewa.

Mallam Umar Namadi ya bayyana cewa, an tallafawa manoman da kayan amfanin gona iri-iri a farashi mai rahusa, da kuma rance mai sauki wanda ya ba su damar noma mai dimbin yawa.

Ya yi nuni da cewa, ana sa ran  samar da tan 800,000 a wannan lokaci na  rani,  da  kuma kwatankwacin hakan  a  daminar bana.

Ya yi nuni da cewa, jihar za ta samar da tan miliyan daya da dubu dari takwas  wanda yayi daidai da kashi 27 bisa dari na shinkafar da ake bukata a duk shekara a Najeriya.

Umar Namadi ya shaida wa manoman cewa, gwamnatinsa na sane da yanayin tsadar man fetur, wanda ke kawo cikas wajen samar da isasshen ruwa yayin nomar rani, inda  ya  yi alkawarin hada hannu da gwamnatin tarayya domin samar musu da tallafi.

Ya kuma yi alkawarin samar da ruwan famfo mai amfani da hasken rana akan farashi mai rahusa ga manoma domin saukaka ayyukansu.

Gwamnan ya yabawa manoman bisa yadda suka nuna jajircewarsu wajen gudanar da sana’arsu, wanda ya bayyana a matsayin abin alfahari.

Da yake jawabi a madadin manoman, Alhaji Dauda Ali Kura ya bayyana cewa, babbar matsalarsu a noman rani ita ce tsadar man fetur, domin shi kadai yana kashe sama da naira miliyan 1 wajen sayen mai a duk mako.

Kura ya yi kira ga Gwamnan da ya kara samar masu da hanyoyin da za su ci gaba da yin noma.

Usman Muhammad Zaria

Labarai

Ilimi1 day ago

KANO: Ungogo Ta Ƙaddamar da Shirin Shigar da Yara Makaranta

Daga Khadijah Aliyu Ƙaramar Hukumar Ungogo ta Jihar Kano ta ƙaddamar da wani shirin wayar da kan jama’a domin shigar...

Labarai1 day ago

Jihar Naija Ta Dauki Matakan Gaggawa Sakamakon Bullar Cutar Ebola A Abuja

Daga Aliyu Lawal Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Nijar ta sanya Cibiyar Ayyukan Gaggawa ta Lafiyar Jama’a (PHEOC) cikin shirin ko-ta-kwana,...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Tarayya Ta Ɗauki Matakan Gaggawa Bayan Tabbatar da Ebola a Birnin Tarayya

Daga Bello Wakili  Gwamnatin Tarayya ta fara aiwatar da matakan gaggawa na kare lafiyar jama’a,  bayan tabbatar da bullar cutar...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Amince Da Fitar Da Naira Biliyan 1.4 Ga Mazabu

Daga Usman Muhammad  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira biliyan 1.4 wajen aiwatar da ayyukan mazabu...

Fasaha2 days ago

Jigawa Ta Ware Naira Miliyan 380 Don Samar da Wutar Lantarki a Cibiyoyin ICT

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da kashe sama da naira miliyan 380 wajen samarwa...

Labarai2 days ago

’Yan Sanda Sun Kama Wanda Ake Zargi da Fashi da Makami A Kano

Daga ABDULLAHI JALALUDDEEN, KANO Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutum da ake zargi da aikata fashi da...

Labarai2 days ago

2027: Ombugadu Ya Yi Alƙawarin kawo Ƙarshen Rashin Tsaro

Daga ALIYU MURAKI, LAFIA Ɗan takara a zaɓen gwamnan Jihar Nasarawa na jam’iyyar PDP, Dr. Emmanuel Ombugadu, ya yi alƙawarin...

Labarai2 days ago

Tajudeen Zai Bayyana Rahoton Ayyukan Tinubu Cikin Kwanaki 14

Daga BELLO WAKILI, Abuja Shugaban Majalisar Wakilai ta Najeriya, Dr. Abbas Tajudeen, ya ce zai bayyana cikakken rahoton nasarorin da...

Labarai2 days ago

Gwamnatin Zamfara Ta Nuna Damuwa Kan Ƙaruwar Hare-Haren ’Yan Bindiga

Daga AMINU DALHATU Gwamnatin Jihar Zamfara ta bayyana matuƙar damuwarta kan ƙaruwar hare-haren ’yan bindiga a wasu sassan jihar a...

Kasuwanci2 days ago

APC Ta Ce Kebbi Na Tare da Tinubu Dari-bisa-Dari

Daga SANI DUTSINMA Babban Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Sanata Abdulazeez Yari, ya ce...

Mafi Shahara