Labarai
Jirgin Farko Na Alhazan Jihar Kwara Ya Isa Kasa Mai Tsarki
Alhazai Dari Uku da goma sha uku da suka fito daga jihar Kwaran Najeriya sun isa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin bana.
Jirgin Air Peace Air ya dauki mahajjatan ne a filin jirgin sama na Ilorin da misalin karfe goma sha daya da rabi na safe zuwa filin jiragen sama na Meddina da ke kasar ta Saudiyya.
Kaddamar da jirgin farkon ya samu halartar Amirul Hajj na jihar Sanata Yahaya Oloriegbe, da wakilin gwamnan jihar, Alhaji Lateef Jiddah, da shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar Farfesa Moshood Jimba da sauran mambobin hukumar.
A jawabinsa, Amirul Hajj na jihar Sanata Yahaya Oloriegbe ya shawarci mahajjatan da su zama jakadu nagari ga jihar da Najeriya baki daya.
Ya kuma bukace su da su yi wa Shugaban kasa da Gwamnan Jihar addu’ar samun nasarar ayyukan da suka sanya a gaba.
Ali Muhammad Rabi’u
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
