Labarai
‘Yan Bindiga Sun Shiga Hannu Yayin Bai Wa Sojoji Cin Hanci A Taraba
Rundunar Sojin Najeriya a jihar Taraba ta ce dakarunta sun kame wasu ’yan bindiga da suka yi musu tayin cin hancin Naira miliyan biyu.
Mataimakin daraktan hulda da jama’a na Runduna ta Shida da ke Jalingo, Laftanar Oni Olubodunde ne ya sanar da kama wadanda ake zargin a kauyukan Chinkai da kuma Sarkin Kudu da ke kananan hukumomin Wukari da Ibbi a jihar.
Ya ce, sojojin sun yi nasarar cafke wasu ’yan ta’adda da suka nemi bayar da cin hancin Naira miliyan biyu domin a sake su.
Ya ce, sojojin sun ki amincewa su karbi cin hancin daga matasan hudu masu shekaru 2o zuwa 28.
Laftanar Oni, ya kara da cewa wadanda ake zargin suna cikin jerin wadanda aka jima ana nema ruwa a jallo saboda hannu kan garkuwa da mutane a Wukari da kewaye.
Babban Birget na 6, Birgediya Kingsley Chidebere Uwa, ya yaba wa sojojin saboda jajircewarsu wajen bin doka da oda.
Ya ce, jajircewarsu ce ta kai ga nasarar da aka samu.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
