Connect with us

Labarai

Majalisar Dokokin Kano Ta Bukaci Gwamnati Ta Tallafawa Wadanda Harin Masallaci Ya Shafa

Published

on

Majalisar dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar  da ta taimaka wa iyalan wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata a harin masallaci da ya faru  a karamar hukumar Gada Gezawa.

Wannan dai ya biyo bayan zaman tattaunawa ne da aka yi a zauren majalisar wanda shugaban majalisar Alhaji Jibril Isma’il Falgore ya jagoranta.

A wani kudiri na gaggawa wanda dan majalisa mai wakiltar mazabar Gezawa Alhaji Abdullahi Yahaya ya gabatar ga  majalisar, ya bayyana cewa mutane 17 ne suka rasu,  yayin da wadanda ke raye ke cikin mawuyacin hali, wanda  a halin yanzu suke samun kulawa a asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano.

Dan majalisar ya bayyana cewa iyalan wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata na bukatar tallafi daga gwamnatin tarayya da na jihohi.

Abdullahi ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, inda ya bukaci hukumomin tsaro da sauran hukumomin da abin ya shafa da su gurfanar da wanda ya aikata laifin.

Sauran wadanda suka goyi bayan kudirin sun hada da wakilan Kiru da Madobi Usman da Sulaiman Mukhtar.

Tun da farko kakakin majalisar Alhaji Jibril Isma’il Falgore ya jajantawa gwamnati da iyalai da daukacin al’ummar jihar bisa wannan mummunan lamari da ya faru,  inda ya yi addu’ar Allah ya ji kan wadanda suka rasu ya kuma ba sauran lafiya.

A wani labarin kuma, Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi gyaran fuska ga kudirin gudanar da kasafin kudi a karatu na biyu.

Shugaban masu rinjaye wanda dan kuma shi ne dan  majalisa mai wakiltar, Dala Alhaji Lawan Hussaini Dala ya yi nuni da cewa dokar tana neman tabbatar da ‘yancin cin gashin kai ga majalisar dokokin Kano kan batutuwan da suka shafi albashi, alawus-alawus, daukar ma’aikata, karin girma da sauransu.

Da yake goyan bayan kudurin, mataimakin shugaban majalisar Alhaji Muhammad Bello Butu Butu ya jaddada cewa, bayan an yi nazari an lura akwai banbance-banbance tsakanin kudurin kula da kudade na majalisar dokokin Kano  da na majalisar  kasar, don haka akwai bukatar gyara.

Majalisar ta dage zamanta zuwa washegari a wani kudiri da shugaban masu rinjaye Lawan Hussaini Dala ya gabatar.

 

Khadija Aliyu

Labarai

Labarai1 day ago

Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu

Daga Nasir Malali  Dakarun Sashe na biyu na Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Yamma, Operation FANSAN YAMMA, sun ceto...

Labarai1 day ago

NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta

Daga Yusuf Zubairu, Kaduna Hukumar Raya Yankin Arewa Maso Yamma ta bayyana dawo da tsaro a matsayin babban fifikonta a...

Labarai5 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi6 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai1 week ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai1 week ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai1 week ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai1 week ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai1 week ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai1 week ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Mafi Shahara