Kasuwanci
Hukumar Samarda Aiki Ta Kasa Ta Koyar Da Matasa Tsarin Bada Horo A Kano.
Hukumar samar da ayyukan yi ta kasa ta tabbatar da aniyar ta wajen magance kalubalen rashin aikin yi tsakanin matasa ta hanyar ba da horon sanin makamar aiki.
Babban Jami’in hukumar NDE a jihar Kano Alhaji Danjuma Shehu ya bayyana haka a lokacin bikin wayar da kan jama’a na shirin koyar da sana’o’i na da aka gudanar a Kano.
Ya ce ayyukan hukumar samar da ayyukan yi ta kasa wajen yakar matsalar rashin aikin yi ta bangaren shirye-shirye guda hudu.
Alhaji Danjuma Shehu ya ci gaba da cewa sassan sun hada da Sashen Ayyukan Jama’a na musamman, Sashen inganta ’yan kasuwa masu kananan sana’o’i, Sashen inganta ayyukan yi a karkara da sashen bunkasa sana’o’i.
Ya ce a karkashin Tsarin Koyan Koyarwa na Kasa, an zabo matasa 20 marasa aikin yi, kuma za a horar da su kan fasahar zamani da Fasahar sana’o’in Cikin Gida.
Alhaji Danjuma Shehu ya lura cewa hukumar ta dauki nauyin horar da masu horar da su don baiwa wadanda aka zabo kwarewa na tsawon watanni uku.
“Babban makasudin horarwar ba wai don baiwa mahalarta damar samun kwarewa ba ne, har ma don gwada iliminsu da kuma dogaro da kansu.”
Wakilin Daraktan Bunkasa Sana’o’i Alhaji Ladan wakili ya bukaci mahalarta taron su yi amfani da wannan dama ta hanyar da ta dace.
ABDULLAHI JALALUDDEEN KANO/Wababe
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
