Labarai
Isra’ila Ta Kashe Plasdinawa Fiye Da 35,000 A Gaza
Israila ci gaba da luguden wuta a Gaza a jiya Lahadi, a yayin da dakarunta ke fafatawa da mayaƙan Hamas a sassa da dama na yankin, inda ma’aikatar lafiyar Hamas ta ce adadin waɗanda suka mutu sakamakon hare-haren ya zarce dubu 35.
Yau sama da watanni 7 da fara wannan yaki tsakanin Isra’ila da Hamas kenan, kuma magatakardan Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres ya buƙaci a tsagaita wuta don samun sukunin aiwatar da ayyukan jinkai, sannan a saki waɗanda ake garkuwa da su ba tare da gindaya wasu sharruɗa ba.
A yayin da al’ummar yankin Gaza ke ci gaba da kasancewa a cikin halin tagayyara, ƙoƙarin samar da yarjejeniyar tsagaita wuta da masu shiga tsakani daga Masar da Qatar ya nuna alamun naƙasu.
A ranar Asabar, shugaban Amurka, Joe Biden ya ce ko a ‘gobe’ ana iya cimma yarjejeniyar tsagaita wuta idan Hamas ta saki waɗanda ta ke garkuwa da su tun daga ranar 7 ga watan Oktoban shekarar da ta gabata da ta kai hari Isra’ila.
A ranar Lahadi, Hamas ta bayyana kalaman Biden a matsayin koma -baya ga tattaunawar, sannan ta ce Fira ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu ya yi gaggawar yin watsi da tattaunawar ta wajen kaddamar da harin ƙasa a Rafah.
A jiya Lahadi, sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken ya ce wannan harin da Isra’ila ta ƙaddamar ta ƙasa zai kawo tasgaro ga doka da oda ne kawai, amma ba zai kawar da Hamas ba.
Rahotanni sun ce luguden wutar da Isra’ila ta yi a cikin dare ya lalata yankuna da dama na Gaza.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai1 day ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai1 day ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
