Connect with us

Labarai

Jami’an Hukumar Hana Shige Da Fice Na Iya Nasu Kokari a Kabi

Published

on

An Bukaci Gwamnatin Tarayya Ta Kula Da Jin Dadin Jami’an Da Ke Aiki Akan Iyakokin Kasan nan

 

Shugaban Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa, Kemi Nandap, ta yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da ya kawo wa hukumar agajin jin dadin jami’an da ke kan iyaka saboda rashin matsuguni na kawo tsaiko wajen gudanar da aikinsu yadda ya kamata.

 

Kwanturola Janar din ta bayyana hakan ne a Kebbi a lokacin da take tantance kan iyakokin jihar domin duba halin da ma’aikatanta ke ciki da kuma kalubalen da ma’aikatanta ke fuskanta a kan iyakokin jihar.

 

Ta kuma jaddada bukatar tabbatar da tsaro a kan iyakokin kasar, domin a sa ido kan abubuwan da ke shigowa daga wajen kasar.

 

“Mun ziyarci kan iyakokin kasa da na ruwa a Kamba, Lolo da Dolekaina, abin da muka gani yana da kyau amma akwai bukatar a yi aiki sosai don tabbatar da tsauraran kan iyakokin, Kebbi wuri ce da ta yi iyaka da kasashe biyu shi ya sa ya zama dole mu yi aiki tukuru.

 

Nandap ta bayyana cewa, suna aiki ba dare ba rana don ƙaddamar da aikin amfani da na’urar zamani e-border wanda zai taimaka wajen bada takardun shige da fice cikin sauki.

 

Ta yabawa kwamandan rundunar dake jihar Kebbi a karkashin kulawar Kwanturola Saidu Muhammed Sabo, bisa yadda hukumar take gudanar da aikinta.

COV/Abdullahi Tukur/Wababe

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai1 week ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara