Kasuwanci
CBN Ya Bai Wa Masu POS Wa’adin Yin Rajista Da Gwamnati
Babban Bankin Najeriya CBN ya bayar da wa’adin ranar 7 ga watan Yulin 2024 ga masu POS su kammala rajista da Hukumar rajistar kamfanoni ta ƙasar CAC.
An bayyana hakan ne lokacin da aka yi wata ganawa tsakanin kamfanonin hada-hadar kuɗi na ƙasa da shugaban hukumar ta rajistar kamfanoni, Hussaini Magaji a Abuja ranar Talata.
Da yake jawabi a wurin taron, shugaban na CAC ya ce wa’adin watanni biyu na yin rajistar ya yi daidai da ka’idojin doka da kuma umarnin babban bankin Najeriya.
Sanarwa da hukumar ta CAC ta fitar ta ce an ɗauki matakin ne domin kare masu mu’amala da kamfanonin hada-hadar kuɗi tare kuma da ƙarfafa tattalin arziki.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
-
Labarai21 hours ago
Dakarun Soji Sun Ceto Mutane 23 Tare Da Kama Lakurawa Hudu
-
Labarai24 hours ago
NWDC Ta Sanya Tsaro A Matsayin Babban Fifikon Ta
