Labarai
Kungiyar AFAN Ta Shirya Taron Bita Ga Manoman Jihar Jigawa
Hadaddiyar kungiyar manoma ta kasa reshen Jihar Jigawa da cibiyar binciken yanayin kasa dake Kaduna sun shirya wa manoma daga wasu kananan hukumomin Jihar Jigawa taron karawa juna sani na yini biyu akan gwajin yanayin karfin kasa kafin manomi ya yi shuka a gona.

Da yake jawabi yayin bude bitar, Farfesa Uzaifatu Karfi na tsangayar aikin gona dake Jami’ar tarayya ta Dutse, ya ce yin gwajin yanayin karfin kasa kafin yin shuka zai tantance wace irin shuka ya dace a yi da za ta bada yabanya mai kyau domin samun albarkar amfanin gona.

A cewar sa, fiye da kashi casa’in na abincin da ake nomawa ko ake sayarwa daga kasa suke fita, don haka ne tsangayar ta baiwa kungiyar AFAN gudunmawar kayayyaki gwaji kuma ta nuna yadda mahalarta taron za su yi amfani da su.

A nasa jawabin, Shugaban kungiyar AFAN a Jihar Jigawa, Injiniya Auwalu Garba Ibrahim, ya ce mahalarta taron zasu je yankunan su daban-daban domin ilimantar da manoma abin da suka koya a lokacin bitar.
Ya kuma godewa Jami’ar da tsangayar koyar da aikin gona saboda taimakawa kungiyar AFAN da sabbin dabarun bunkasa noma da cin ribar noma a jihar.

Mahalarta taron sun nuna jin dadin su tare da godewa jami’ar da kuma kungiyar AFAN bisa shirya bitar, wadda suka ce sun karu sosai a fannin inganta noma.
Usman Mohammed Zaria
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
