Labarai
An Kashe Jagoran Harin NDA Da Sace Daliban Birnin Yauri

Sojoji sun kashe kasurgumin dan bindiga, Boderi, wanda ya kitsa harin da aka kai makarantar horas da sojoji ta NDA da ke Kaduna.
Boderi ne kuma ya kitsa hari da kuma sace dalibai a Jami’ar Greenfield da ke jihar, da kuma ’yan matan makarantar sakandaren Birnin Yauri da ke Jihar Kebbi, kamar yadda kakakin rundunar, Manjo-Janar Onyema Nwachukwu, ya sanar.
Sanarwar ta ce cewa a ranar Laraba aka kashe Boderi ne tare da wani shugaban ’yan bindiga mai suna Bodejo a kan hanyar Bada–Riyawa da ke kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari.
“Majiyoyin leken asiri sun ba da rahoton cewa an kashe kasurgumin dan bindiga Boderi wanda ya kitsa sace daliban Birnin Yauri, Jami’ar Greenfield da kuma NDA, tare da wani mai suna Bodejo.
“Ana ci gaba da kokarin tabbatar da hakan ta hanyar amfani da wasu hanyoyi,” in ji sanarwar.
A cewarsa, kun kwato babura 19 da ’yan ta’addan suka gudu suka bari da wasu abubuwa, kuma an kona su.
a wani samame na daban da sojoji suka kai a yankin, “’yan ta’addan da suka yi amfani da shanu a matsayin garkuwa, sun bude musu wuta, amma suka mayar da martani cikin gaggawa.
“A yayin musayar wutar ta kusan awa daya, sojoji sun kashe biyu daga cikin ’yan ta’addan tare da kwato bindiga kirar AK 47 guda 1, da sauran abubuwa.
“Sai dai kuma an kashe wasu daga cikin dabbobin satan da da ’yan ta’addan ke amfani da su a matsayin garkuwa.
-
Labarai3 days agoIran ta Tabbatar da Kisan Ayatollah Khamenei a Hare-haren Amurka da Isra’ila
-
Labarai4 days agoMajalisar Dokokin Jihar Kaduna Ta Amince da Kasafin Kudin Kananan Hukumomin Jihar na 2026
-
Labarai4 days agoAzumin Ramadan: Shugaban Karamar Hukumar Birnin Kudu Ya Bada Tallafin Kudi ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoUwargidan Gwamnan Zamfara Ta Kaddamar da Rabon Tallafin Ramadan ga Marasa Galihu
-
Labarai6 days agoWani Bam Kirar Hannu Ya Fashe a Kan Hanyar Gusau Zuwa Funtua
-
Labarai3 days agoBankin Raya Kasashen Afirka Zai Samar da Shirin Bunƙasa Aikin Noma a Jigawa
-
Labarai3 days agoGwamnatin Jigawa ta Gargadi ‘Yan Kwangila Kan Ingancin Abincin Ramadan
-
Labarai3 days agoMasarautar Hadejia ta Raba Zakkar Kayan Amfanin Gona da Dabbobi a Garin Unik
