Kasuwanci
Dangote Ya Karya Farashin Man Dizel
Matatar man Aliko Dangote ta sanar da ƙara rage farashin man dizel zuwa naira 1,000 kan kowacce lita.
A cikin wata Sanarwa da kamfanin ya Fitar ranan Talata ya ce ana sa ran ”rage farashin man dizel ɗin zai yi tasiri sosai a dukkan ɓangarorin tattalin arziki da kuma rage hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya.”
A watan Janairu ne matatar man Dangote ta fara samar da man dizel da na jiragen sama.
Tun daga lokacin matatar take sayar da man dizel a kan farashi mai rahusa na Naira 1,200 a kowace lita, kimanin kashi 30 cikin 100 na ragin farashin kasuwa da ya kai kusan Naira 1,600 kan kowace lita.
Kamfanin ya ɗaura ɗamarar fara samar da tataccen man fetur tare da samun ƙarin ganga miliyan ɗaya na ɗanyen man da Kamfanin Mai na Nijeriya (NNPC Ltd) ya kawo.
A farkon watan ne kamfanin ya fara fitar da albarkatun man fetur ga kasuwannin cikin gida.
-
Ilimi6 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai7 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai7 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai7 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Labarai7 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoMasu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki
-
Labarai5 days agoGwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York
