Labarai
An Bukaci Masu Kula da Lafiyar Al’umma Su Rike Ka’idojin Aiki
An bukaci masu aikin kula da lafiyar al’umma da su kasance masu bin ka’idojin sana’arsu tare da kiyaye martabar aikin, domin inganta ayyukan kiwon lafiya a Najeriya.
Magatakardar Hukumar Rajistar Masu Aikin Kula da Lafiyar Al’umma ta Najeriya, Farfesa Bashir Idris Lifidi Jama’a, ya bayyana haka ne yayin da yake tsokaci kan bikin Makon Lafiyar Al’umma na bana.
Farfesa Bashir Idris Lifidi Jama’a ya ce ana shirya bikin ne duk shekara da nufin karfafa gwiwar masu aikin kula da lafiyar al’umma, tare da tunatar da su muhimmiyar rawar da suke takawa wajen ci gaban kasa.
Magatakardar ya bayyana cewa ya zama wajibi ga masu aikin kula da lafiyar al’umma da sauran masu ruwa da tsaki a bangaren kiwon lafiya su rika bin sabbin ka’idojin da aka gindaya, domin inganta ayyukansu da tabbatar da samar da ingantaccen kiwon lafiya ga al’umma.
Ya kuma yi kira ga gwamnatocin jihohi da na tarayya da su kara tallafa wa bangaren kiwon lafiya, ta hanyar samar da kayan aiki da sauran abubuwan da ake bukata, tare da inganta yanayin aiki ga ma’aikatan lafiya, domin samun ci gaba mai ma’ana a fadin kasar.
By Maryam Idris
-
Labarai5 days agoJigawa: Grand Khadi Ya Fara Rangadin Kotunan Shari’a
-
Labarai3 days agoNIAS Ta Karrama Namadi Bisa Bunƙasa Harkar Kiwo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Kebbi Ta Kammala Shirye-shiryen Tarbar Tinubu
-
Labarai4 days agoGobara Ta Lalata Shaguna 10 A Jihar Kwara
-
Labarai4 days agoShugaban Majalisar Kano Ya Ƙaddamar Da Sabon Ofishin ’Yan Sanda A Rogo
-
Labarai1 day agoINEC Ta Ƙaddamar Da Kwamitin Wayar Da Kai Ga Masu Zaɓe A Kaduna
-
Labarai5 days agoZa a Gabatarda Zaben Kananan Hukumomi a 2027 a Kaduna
