Connect with us

Labarai

Tinubu Ya Gargadi ’Yan Siyasa Kan Tashin Hankali Gabanin Zaɓen 2027

Published

on

Daga Bello Wakili 

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gargaɗi ’yan siyasa da magoya bayansu kan guje wa tashin hankali, yayin da harkokin siyasa ke ƙamari gabanin babban zaɓen shekarar 2027.

A cikin wata sanarwa, Shugaban Ƙasar ya yi Allah-wadai da rahotannin tashin hankali a wasu tarukan siyasa a sassa daban-daban na ƙasar, yana mai jaddada cewa babu gurbin tashin hankali a harkokin yaƙin neman zaɓe a tsarin dimokuraɗiyya.

Ya buƙaci jam’iyyun siyasa da magoya bayansu da su mayar da hankali kan manufofi da shirye-shiryen da za su inganta rayuwar al’umma da ci gaban ƙasa.

Shugaba Tinubu ya sake jaddada ƙudurinsa na tabbatar da gudanar da zaɓe cikin lumana, ’yanci da adalci, tare da kira ga shugabannin siyasa da su nuna haƙuri da ɗaukar nauyi.

Ya bayyana cewa bambancin ra’ayin siyasa da burin neman mulki bai kamata su mayar da ’yan Najeriya maƙiya ga juna ba.

Shugaban Ƙasar ya kuma umarci hukumomin tsaro da su ɗauki matakan da suka dace wajen tunkarar duk masu ƙoƙarin kawo cikas ga zaman lafiyar al’umma.

Ya tabbatar wa jam’iyyun siyasa da ‘yan takara da cewa za a samar musu da isasshen tsaro domin gudanar da yaƙin neman zaɓe cikin ‘yanci a kowane yanki na ƙasar ba tare da tsoratarwa ba.

Sai dai Tinubu ya yi gargaɗin cewa gwamnatinsa ba za ta lamunci halayen rashin ɗa’a daga ‘yan siyasa da magoya bayansu ba, inda ya umarci hukumomin tsaro da su tunkari masu tada zaune tsaye da sauran ayyukan da suka saɓa wa dimokuraɗiyya.

Fassara: Safiyah Abdulkadir 

Labarai

Labarai13 hours ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ware Sama Da Naira Biliyan 1 Don Bunƙasa Kiwo Da Sana’o’i

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe naira biliyan 1.124 domin ginawa da gyara cibiyoyin kiwo...

Labarai13 hours ago

Tinubu Ya Gargadi ’Yan Siyasa Kan Tashin Hankali Gabanin Zaɓen 2027

Daga Bello Wakili  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gargaɗi ’yan siyasa da magoya bayansu kan guje wa tashin hankali,...

Labarai13 hours ago

Jigawa Ta Amince Da Naira Miliyan 570 Don Inganta Abinci Mai Gina Jiki

Daga Usman Muhammad Zaria  Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da ware naira miliyan 570 a matsayin tallafin haɗin...

Labarai14 hours ago

Jigawa Ta Ware Sama Da Naira Biliyan 1 Ga Ayyukan Samar Da Ruwa

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta amince da kashe naira biliyan 1.116 domin gudanar da ayyukan samar da...

Labarai2 days ago

Sauye-sauyen Da Tinubu Ya Samar Ya Haifar Da Cigaba A Jihohi – Namadi

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan matakan da...

Labarai2 days ago

Jigawa Ta Yi Nazarin Sabbin Tsare-tsaren Masaukin Alhazai A Saudiyya

Daga Usman Muhammad Zaria Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce tana nazarin hanyoyin inganta jin daɗin alhazai...

Labarai3 days ago

Kano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400

Daga Khadijah Aliyu  Wata kotu a Jihar Kano ta bayar da umarnin lalata buhunan fulawa sama da 400 da suka...

Labarai4 days ago

Tinubu Ya Jaddada Ƙudurin Samar Da Ci Gaba A Jigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada ƙudurin gwamnatinsa na ci gaba da aiwatar da...

Labarai4 days ago

Shugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus

Daga Isma’il Adamu  Babban Manajan gidan talabijin na Jihar Katsina (KTTV), Abba Zayyan, ya miƙa takardar murabus daga muƙaminsa a...

Labarai4 days ago

Namadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, ya bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya kai musu...

Mafi Shahara