Labarai
Jigawa Ta Yi Nazarin Sabbin Tsare-tsaren Masaukin Alhazai A Saudiyya
Daga Usman Muhammad Zaria
Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Jigawa ta ce tana nazarin hanyoyin inganta jin daɗin alhazai ta hanyar sanin sabbin hanyoyin bunƙasa gine-ginen gidaje da ababen more rayuwa a Saudiyya.
Shugaban hukumar, Alhaji Ahmed Umar Labbo ne ya bayyana hakan bayan halartar taron baje kolin harkokin aikin Hajji karo na shida, wanda aka kammala a birnin Jidda na ƙasar Saudiyya.
Labbo ya ce halartar taron ya ba hukumar damar sanin sabbin tsare-tsare da ake amfani da su wajen samar da masauki, tsara birane da sauran abubuwan more rayuwa da suka shafi gudanar da aikin Hajji.
Ya kuma kai ziyara wajen baje kolin gidaje na Madina, inda ya duba wani babban tsarin gina gidajen zama tare da wasu mahalarta daga Saudiyya.
A cewarsa, baje kolin ya nuna dabarun bunƙasa gidajen zama, ababen more rayuwa da tsarin tsara birane na zamani, lamarin da ya ba da haske kan irin ci gaban da ake samu a Saudiyya.
Labbo ya ce sanin irin waɗannan sabbin abubuwa na ƙasashen duniya na da muhimmanci ga masu kula da harkokin Hajji a jihohi, musamman wajen gano hanyoyin inganta masaukin alhazai da ƙwarewarsu gaba ɗaya yayin gudanar da ibadar Hajji.

Ya bayyana cewa ilimin da aka samu daga taron zai taimaka wajen ƙarfafa shirye-shirye, inganta ayyukan hidima da gano ƙarin hanyoyin inganta jin daɗin maniyyata a Jihar Jigawa.
Labbo ya ƙara da cewa taron baje kolin na Hajji karo na shida ya haɗa masu ruwa da tsaki daga ƙasashe daban-daban domin tattauna batutuwa da suka shafi aikin Hajji, ƙulla hulɗa a tsakanin ƙwararru da kuma gabatar da sabbin dabaru a harkokin Hajji da Umara.
Ya ce halartar irin waɗannan taruka na bai wa hukumomin jin daɗin alhazai na Najeriya damar fahimtar sauye-sauyen da ake samu a harkokin gudanar da Hajji, ƙulla hulɗar aiki da kuma sanin sabbin abubuwan da ke faruwa a Saudiyya.
Yayin da ake tunkarar shirye-shiryen aikin Hajjin 2027, Labbo ya ce abubuwan da aka koya za su taimaka wajen nazarin sabbin hanyoyin samar da masauki, daidaita ayyuka da inganta hidimar alhazai a Jihar Jigawa.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Labarai4 days agoJigawa Ta Amfana Da Ayyukan Gwamnatin Tinubu – Abdulaziz
-
Labarai5 days agoTsoffin Gwamnonin Jigawa Sun Yaba Wa Nasarorin Gwamna Namadi
-
Labarai5 days agoNamadi Ya Ƙaddamar Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen APC Na 2027
-
Labarai5 days agoYankin Funtua Sun Yi Fitowar Farin Dango A Yakin Neman Zaɓe Na APC- Hamza Faskari
-
Labarai4 days agoMajalisar Kano Za Ta Karɓi Kasafin Kuɗin Shekarar 2027
-
Labarai2 days agoNamadi Ya Miƙa Buƙatu Uku Ga Tinubu Kan Ci gaban JiharJigawa
-
Labarai2 days agoKano: Kotu Ta Umarci A Lalata Buhunan Fulawa Sama Da 400
-
Labarai2 days agoShugaban Gidan Talabijin Na Katsina Abba Zayyan Ya Yi Murabus
