Ilimi
An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
Daga Khadijah Aliyu
Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban a faɗin ƙaramar hukumar.
An gudanar da rabon kayan a Hukumar Kula da Ilimin Firamare ta Gwarzo, a wani ɓangare na ƙoƙarin ƙaramar hukumar na tallafa wa ilimin firamare da inganta yanayin koyo da koyarwa.
Da yake wakiltar Shugaban Karamar Hukumar, Dakta Mani Tsoho Gwarzo, Shugaban Majalisar Karamar Hukumar Gwarzo, Ahmad Shehu, ya ce samar da kayan karatu da sauran abubuwan da ɗalibai ke buƙata zai taimaka wajen ba su damar samun ilimi a yanayi mai kyau.
Sakataren Ilimi na yankin, Ashiru Lawan, ya ce kayan makaranta na taimakawa wajen tabbatar da ladabi, tsafta da mutunci tsakanin ɗalibai, tare da ƙarfafa musu jin cewa suna cikin makaranta.
Shugaban Gundumar Gwarzo, Alhaji Bello Abubakar, ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kano da Karamar Hukumar Gwarzo bisa wannan shiri na tallafa wa ilimi.
An miƙa kayan makarantar guda 20,243 ga shugabannin makarantun firamare domin su rarraba su ga ɗaliban da suka cancanta a faɗin ƙaramar hukumar.
Wasu daga cikin waɗanda suka amfana, Ismail Sani Ismail da Fatima Muhammad na Makarantar Gwarzo Model Science, sun nuna godiyarsu tare da alkawarin amfani da kayan yadda ya kamata da kuma mayar da hankali kan karatunsu.
Makarantun firamare guda 191 ne ake sa ran za su amfana da wannan rabon a faɗin Karamar Hukumar Gwarzo.
Fassara: Safiyah Abdulkadir
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
-
Labarai7 days agoGwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya
