Connect with us

Labarai

Gwamnatin Jigawa Ta Amince da Ƙarin Ayyuka Kan Ginin Hedikwatar Injinan Noma

Published

on

Daga Usman Muhammad Zaria

Majalisar Zartarwa ta Jihar Jigawa ta amince da ƙarin ayyuka na ginin hedikwatar Kamfanin Injinan Noma na jihar da ke Dutse kan kuɗi sama da naira miliyan 155.3, lamarin da ya ƙara yawan kuɗin kwangilar zuwa sama da naira miliyan 906.

Kwamishinan Yaɗa Labarai, Matasa, Wasanni da Al’adu na jihar, Alhaji Sagir Musa Ahmed ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Fadar Gwamnati da ke Dutse.

Ya ce amincewar majalisar ta yi daidai da ƙudirin Gwamna Umar Namadi na ƙarfafa fannin noma, ta hanyar inganta ayyukan amfani da injinan noma da samar da ingantattun gine-ginen more rayuwa da za su ƙara inganta gudanar da aiki, haɗin kai da kuma isar da ayyukan noma a faɗin jihar.

Ya ƙara da cewa ana sa ran sabon ginin hedikwatar kamfanin zai kasance cibiyar tsara shirye-shirye, gudanarwa, sa ido da kuma aiwatar da manufofi da shirye-shiryen injinan noma a jihar.

Alhaji Sagir Musa Ahmed ya bayyana cewa ginin zai samar da isassun ofisoshi da wuraren aiki na zamani ga ma’aikatan fasaha da na gudanarwa da ke da alhakin bunƙasa harkokin injinan noma a faɗin jihar.

A cewarsa, majalisar ta nuna kwarin gwiwar cewa aikin zai taimaka matuƙa wajen cimma manufofin sauya fasalin aikin noma na jihar ta hanyar samar da ingantaccen tsarin gudanarwa da kula da ayyukan injinan noma tare da tabbatar da ingantaccen isar da ayyuka ga manoma.

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara