Kasuwanci
Hukumar Tace Fina-Finai Ta Kano Ta Dakatar Da Jaruman Kannywood Biyu Kan Bidiyon Rashin Ɗa’a
Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano ta dakatar da wasu jaruman Kannywood biyu, Amina Uba Hassan da Adam Garba, daga dukkan harkokin fim a jihar na tsawon shekara guda, bisa dalilin sakin wani bidiyo da hukumar ta bayyana a matsayin wanda bai dace da ɗa’a ba.
Hukumar ta ce matakin ya biyo bayan yaduwar bidiyon da ake zargin ya shafi jaruman biyu, wanda ya jawo cece-kuce da kuma tashin hankali a wasu sassan al’ummar jihar Kano.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar, Abdullahi Sani, ya fitar a madadin Babban Sakataren hukumar, Abba El-Mustapha.

Sanarwar ta ce matakin dakatarwar ya yi daidai da ikon hukumar na tsara da kula da harkokin nishaɗi tare da tabbatar da bin dokokin tace fina-finai a jihar Kano.
“Hukumar na da ikon doka na dakatar da duk wani jarumi ko jaruma da aka samu ya karya ƙa’idojin tace fina-finai a yankin Jihar Kano,” in ji sanarwar.
Hukumar ta kuma yi gargadi cewa duk wanda ya ƙi bin wannan umarni na dakatarwa zai fuskanci matakin shari’a da sauran hukunci da doka ta tanada.
Haka kuma, Babban Sakataren hukumar, Abba El-Mustapha, ya yi kira ga masu ruwa da tsaki a masana’antar Kannywood da su guji duk wani abu da zai iya ɓata sunan masana’antar fina-finan Hausa.
Ya buƙaci masu shirya fina-finai da daraktoci da sauran masu harkar fim da su tabbatar sun bi wannan umarni sosai, yana mai cewa hukumar ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaukar mataki kan duk wanda ya karya ka’ida.
A ‘yan shekarun nan, Hukumar Tace Fina-Finai ta Kano na ƙara ƙaimi wajen kula da abubuwan da ake samarwa a masana’antar Kannywood, musamman abubuwan da ake ganin sun saɓa da al’ada da ɗabi’un al’ummar jihar.
Rel/Khadijah Aliyu
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
