Labarai
Gwamna Namadi Ya Bayyana Alhininsa Bisa Rasuwar Tsohon Dan Majalisa Abba Anas Adamu
Daga Usman Muhammad Zaria
Gwamnan Jihar Jigawa, Umar Namadi, ya bayyana matukar alhininsa kan rasuwar tsohon dan majalisar wakilai ta tarayya, Alhaji Abba Anas Adamu, inda ya ce rasuwarsa babban rashi ne ga Jihar Jigawa da ma kasa baki daya.
Gwamnan ya bayyana hakan ne jim kadan bayan halartar sallar jana’izar marigayin da aka gudanar a Kano a yau Talata, 12 ga watan Mayun 2026, inda ya jajantawa iyalai, da abokan arziki bisa wannan babban rashi, tare da yi masa addu’ar samun rahama.
Gwamna Namadi ya bayyana marigayi Abba Anas Adamu a matsayin jajirtacce, wanda ya sadaukar da wani bangare mai muhimmanci na rayuwarsa wajen yi wa al’ummarsa hidima.

Ya kuma ce marigayin ya taka muhimmiyar rawa a fannoni daban-daban na hidimar jama’a, ciki har da kasancewarsa tsohon dan majalisar wakilai ta tarayya, tsohon shugaban karamar hukumar Guri, tsohon kwamishina a Jihar Jigawa, sannan kuma gogaggen malami.
A cewarsa, za a rika tunawa da marigayin musamman saboda tawali’unsa, da jajircewarsa wajen tabbatar da dimokuradiyya, da gudummawar da ya bayar wajen bunkasa harkokin siyasar Jihar Jigawa.
Gwamna Namadi ya roki Allah Madaukakin Sarki da Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya sanya shi a Aljannatul Firdaus, sannan Ya bai wa iyalansa, da abokan arziki, da ma abokan siyasarsa da al’ummar Jihar Jigawa juriyar jure wannan babban rashi.
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
