Labarai
MD Ya Zargi Shugaban Ƙungiya Da Katsalandan
Hukumar Raya Kogin Neja ta Ƙasa ta zargi wani shugaban ƙungiyar ma’aikata da haddasa rikici domin dakile binciken zargin almundahanar kuɗi da ake yi masa.
Manajan Daraktan hukumar, Olushola Olumoroti, ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a Ilorin ta Jihar Kwara. Ya ce Mudi Raji, tsohon Manajan yankin Ilorin kuma shugaban ƙungiyar ma’aikatan noma ta jihar Kwara, ya tunzura ma’aikata suka tare kofar hukumar tare da hana gudanar da aiki.
Olumoroti ya ce ana binciken Raji da wasu ma’aikata kan zargin karkatar da kuɗaɗen gwamnati da rashin mayar da kudaden shiga gwamnati. Ya ƙara da cewa kwamitoci uku sun same su da laifi tare da bada shawarar hukunci da karɓo kuɗaɗen da suka ɓata.
Sai dai ya ce zanga-zangar da aka yi na da nufin hana sabon kwamitin bincike gudanar da aikinsa, yana mai cewa gwamnati ba za ta lamunci tashin hankali da cin zarafin ma’aikata ba.
Ali Muhammad Rabi’u/Kwara
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai6 days agoMajalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari
