Labarai
Shugaba Tinubu Ya Isa Kenya Don Halartar Taron Koli Na Afirka Da Faransa
Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya isa Nairobi, babban birnin Kenya gabanin taron ƙoli na Afirka da Faransa da za a shafe yini biyu ana yi.
Shugaba Tinubu ya samu tarba daga jami’i a gwamnatin Kenya, Musalia Mudavadi wanda kuma shi ne sakataren da ke kula da harkokin da suka shafi ƙasashen ƙetare.

Akwai kuma Ministar harkokin waje ta Najeriya, Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu da Jakadan Kenya a Najeriya, Amb. Isaac Parashina.
Taron zai ƙara ƙarfafa ƙudirin Najeriya na zurfafa alaƙa da kuma haɗin kai da sauran ƙasashen Afirka da kuma Faransa.

Bello Wakili/Abuja
-
Ilimi5 days agoAn Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo
-
Labarai6 days agoGwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027
-
Labarai7 days agoADC Ta Kaddamar da Yakin Neman Zabe a Daura, Ta Jaddada Matsayinta Kan Tallafin Man Fetur
-
Labarai6 days agoUNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina
-
Labarai6 days agoNSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara
-
Labarai6 days agoMataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya
-
Ilimi7 days agoZamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta
-
Labarai7 days agoGwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya
