Connect with us

Labarai

Gwamnan Jihar Neja Ya Ba Da Umarnin Gyaran Gaggawa A Sansanin NYSC Da Ke Paiko

Published

on

Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umar Bago, ya umarci Sakataren Gwamnatin Jihar da ya hada kai da Ma’aikatun Ayyuka, Matasa da Ci gaban Al’umma domin tabbatar da gyaran gaggawa na rufin gine-ginen da iska ya kware da kuma wasu gine-gine da suka lalace a sansanin masu yi wa kasa hidima na National Youth Service Corps da ke Paiko.

Umarnin na kunshe ne cikin wata sanarwa da babban sakataren yada labaran gwamnan, Bologi Ibrahim, ya fitar ga manema labarai a Minna, inda ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici da damuwa.

Tuni dai tawagar tantance barnar, wadda ta hada da Kwamishinar Ilimi, Dakta Hadiza Asabe Mohammed, Kwamishinan Matasa da Ci gaban Al’umma, Jacob Baba Yisa, Darakta Janar na National Youth Service Corps, Birgediya Janar Olakunle Oluseye Nafiu, da kuma kodinetan NYSC na jihar, Misis Martina Shuaibu-Ibrahim, suka ziyarci wurin domin duba irin barnar da aka yi.

Gine-ginen da abin ya shafa sun hada da dakunan kwanan maza masu yi wa kasa hidima, babban dakin taro na ayyuka daban-daban, kicin, gidajen ma’aikata da kuma wasu sassan gidan kodinetan jihar.

Gwamna Umar Bago ya bayyana cewa babu shakka wannan lamari ya jefa masu yi wa kasa hidima da jami’an sansanin cikin wani hali na rashin jin dadi, yana mai cewa gyaran gaggawar da za a yi wa wuraren da suka lalace zai taimaka wajen bai wa matasan damar ci gaba da gudanar da atisayen tantancewa cikin kwanciyar hankali.

Haka kuma, ya yaba wa tawagar tantancewar da kuma shugaban makarantar sakandaren Abubakar Dada Secondary School da ke Paiko bisa hadin gwiwar da suka yi na samar da azuzuwa a matsayin matsuguni na wucin gadi ga matasan da lamarin ya shafa.

Gwamnan ya kuma sake tabbatar wa da NYSC cewa gwamnatinsa a shirye take domin tabbatar da tsaro da walwalar dukkan masu yi wa kasa hidima a fadin jihar.

Aliyu Lawal/Minna

Labarai

Labarai4 days ago

Gwamna Dauda Lawal Zai Halarci Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya A New York

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, zai halarci zama na 81 na Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya...

Ilimi5 days ago

An Raba Kayan Makaranta 20,243 Ga Ɗalibai A Gwarzo

Daga Khadijah Aliyu  Karamar Hukumar Gwarzo ta Jihar Kano ta raba kayan makaranta guda 20,243 ga ɗaliban makarantun firamare daban-daban...

Labarai6 days ago

Gwamnatin Jigawa Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Shirye-shiryen Hajjin 2027

Daga Usman Muhammad Zaria  Gwamnatin Jihar Jigawa ta sake jaddada aniyarta ta ci gaba da aiki kafada da kafada da...

Labarai6 days ago

Mataimakin Shugaban Ƙasa Shettima Ya Dawo Najeriya Bayan Taron BRICS A Indiya

Daga Bello Wakili, Abuja Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya dawo Najeriya bayan ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a...

Labarai6 days ago

UNICEF Ta Ƙaddamar Da Shirin Koyar Da ’Yan Mata Sana’o’i A Katsina

Daga Isma’il Adamu, Katsina Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, UNICEF, tare da haɗin gwiwar Hukumar Ilimin Firamare ta...

Labarai6 days ago

NSCDC Ta Kama Mutane Tara Kan Zargin Safarar Miyagun Ƙwayoyi Da Sata A Zamfara

Daga Aminu Dalhatu, Gusau Hukumar Tsaro Farin kaya ta Najeriya, NSCDC, reshen Jihar Zamfara, ta kama wani mutum mai shekaru...

Labarai6 days ago

Majalisar Dokokin Kano Ta Buƙaci Kammala Aikin Faɗaɗa Hanyoyin Ban-ruwa Na Madatsar Ruwan Watari

Daga KHADIJAH ALIYU, Kano Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi kira ga gwamnatin jihar da ta tabbatar da kammala aikin...

Labarai6 days ago

Masu Amfana Da Shirin KWACReSAL A Kwara Sun Faɗaɗa Gonaki

Daga ALI MUHAMMAD RABIU Shirin Ƙarfafa Juriya Ga Sauyin Yanayi A Yankunan Busassun yankuna na Jihar Kwara, KWACReSAL, ya fara...

Ilimi7 days ago

Zamfara Ta Kaddamar Da Shirin Shigar Da Yara Makaranta

Daga Aminu Dalhatu  Hukumar Ilimin Bai-daya ta Jihar Zamfara, ZSUBEB, ta kaddamar da shirin shigar da yara makaranta na shekarar...

Labarai7 days ago

Gwamnan Kebbi Ya Yabi WAMY Kan Jinya Kyauta Ga Marasa Lafiya

Daga Sani Dutsinma Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya yaba wa Ƙungiyar Matasa Musulmi ta Duniya (WAMY) kan shirya aikin...

Mafi Shahara